Aisha Buhari ta sa a tsare dogarin ta bisa zargin lamushe mata N2.5bn

Aisha Buhari ta sa a tsare dogarin ta bisa zargin lamushe mata N2.5bn

Uwargidan Shugaban Kasa Muammadu Buhai, Hajiya Aisha ta bayar da umurni kan wa a tsare mata babban dogarin ta, sannan a bincike shi akan zargin lamushe mata da kudi da yayi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Wannan kudi dai kamar yadda aka rahoto bayyana kudi ne masu yawa domin sun kai kimanin naira biliyan 2.5.

Aisha ta zargi dogarin nata ne da lamushe wadannan kudade wanda ‘yan siyasa ne suka rika bata kyauta ta hannun sa kamar yadda ta zarge shi.

Dogarin mai suna Sani Baba-Inna ya bayyana cikin wannan badakalar ne bayan ya musanta karbar wadannan kudade da Aisha ke zargin sa da yn sama da fadi akai.

Aisha ta umarci sufeton ‘yan sanda Ibrahim Idris da ya gaggauta gudanar da bincike akai.

Aisha Buhari ta sa a tsare dogarin ta bisa zargin lamushe mata N2.5bn
Aisha Buhari ta sa a tsare dogarin ta bisa zargin lamushe mata N2.5bn
Asali: Depositphotos

Nan da nan kuwa sufeto janar Idris ya tasa keyar ADC Baba-Inna inda aka fara gudanar da bincike akai.

Sai dai kuma hakan su bai cimma ruwa ba domin ba a samu Baba-Inna da irin wadannan kudade ba.

Da aka binciki asusun ajiyar sa ta banki sai aka ga naira 30,000 ne ya rage a ciki sannan ko a gidan sa ma an samu naira 1,200 ne kacal da ya ajiye wa mai dakin sa kudin cefane.

Ba a dai samu komai tare da wannan bawan Allah ba. Duk da haka Aisha tace bata gamsu ba sannan ta zargi suma ‘yan sandan cewa sun hada baki ne da Baba-Inna domin cikin wadanda ake zargi da yi wa Aisha kyautar kudi har da sufeto janar Ibrahim Idris.

Ko da yake tuni idris ya karyata haka cewa babu abin da ya taba hada shi da wannan ADC da har ya bashi kudi ya ba Aisha.

KU KARANTA KUMA: APC a Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida

Daga nan kuma sai Aisha ta fusata ta garzaya ofishin SSS, inda a yanzu haka bincike ya nuna cewa Bana-Inna na nan a tsare a wajen su.

Uwargidan Baba-Inna ta tabbatar wa cewa mijin ta na can a tsare bata san inda yake ba kamar yadda jaridar Premium Timesta ruwait .

Shiko kakakin rundunar ‘Yan sanda Moshood Jimoh cewa yayi bashi da cikakken bayanai kan wannan badakala kamar yadda na hukumar SSS ya fadi shima.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel