Tinubu ya caccaki Tsohon Shugaban 'Kasa, Obasanjo, kan Wasiƙun sa ga Shugaba Buhari
Mun samu rahoton cewa kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyya APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya yi kaca-kaca da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, dangane da rashin goyon kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake neman takarar kujerar sa.
Tinubu yake cewa, Obasanjo da daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP da ta jagoranci kasar nan har na tsawon shekaru 16 ba tare da wani abun zo a gani ba.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Tinubu ya bayyana hakan ne cikin birnin Ikot-Ekpene na jihar Akwa Ibom yayin yiwa Sanata Godswill Akpabio lale maraba yayin sauyin shekar sa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya gargadi masu kokarin hambarar da shugaba Buhari daga shugabancin kasar nan akan su sauya tunani da salon su domin kuwa "wutsiyar Rakumi tuni ta yi nisa da kasa."
Tinubu ya yi fata-fata da tsohon shugaban kasar musamman dangane da budadan wasiku da rika rubutawa shugaba Buhari inda yake suka da caccakar gwamnatin sa.
KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta na yiwa Zaɓen 2019 riƙo tamkar wani lamari na Gaggawa - Dogara
Yake cewa, har yanzu tsohon shugaban kasar bai waye ba ta fuskar fasahar zamani da a yanzu lokaci na rubuta wasika cikin takarda ya yi nisa da tafiya sakamakon amfani da hanyoyin sadarwa da kuma yanar gizo wajen aika sakonni.
Legit.ng ta fahimci cewa, Tinubu ya bayyana fushin sa gami da damuwa kwarai da aniyya dangane da rashin tsinanawa kasar nan komai da jam'iyyar PDP ta yi har na tsawon shekaru 16 na mulkin kama karya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng