Ra'ayi riga: Anya Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa taka leda ba gwari yayi ba?

Ra'ayi riga: Anya Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa taka leda ba gwari yayi ba?

- Suyin sheka ba ga 'yan siyasa ya tsaya ba har ga 'yan wasan kwallon kafa

- Ahmed Musa ya sauya sheka zuwa wata kungiya a kasar Larabawa

- Sai dai hakan ya haifar da mabambantan ra'ayi ga magoya bayansa

Dan wasan gaba na Najeriya dake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta kasar Ingila ya sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya, sai dai hakan ya bar magoya bayansa da dama cikin bayyana sabanin ra'ayi.

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Ahmed Musa ya kasance dan wasa mafi tsada da kungiyarsa ta Leicester ta taba siya akan kudi £16.6. Sai dai za’a iya cewa Musa bai je kungiyar ta Leicester a sa'a ba, inda ya kasa tabuka abin azo-a-gani.

Daga bisani kungiyar ta bayar da shi aro ga kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow dake kasar Russia, wanda a nan ne ya cigaba da nuna bajinta kamar yadda ya saba.

Musa ya nuna bajinta matukata gaya a gasar cin kofin Duniya na 2018 da aka kammala, musamman a karawar Najeriya da kasar Iceland, inda ya samu nasarar zura kwallaye har guda biyu wanda kwallonsa guda daga ciki ta shiga cikin jerin kwallayen da za’a bawa kyautar mafi kyawu.

KU KARANTA: Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa

Jim kadan bayan kammala gasar kofin Duniya Musa ya koma kungiyarsa ta Leicester City domin cigaba da daukar atisaye, wanda daga bisani kungiyar tasa ta cimma yarjejeniya da Al-Nassr wajen sayar da dan wasan nata.

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Shima dai dan wasan ya bayyana jin dadinsa wajen ganin ya samu damar sauya sheka zuwa kungiyar ta Al-Nassr kamar yadda ya bayyana a shafin sada zumuntarsa na Instagram "Ina matukar godiya da jin dadi da na samu wannan dama na kasancewa daya daga cikin yan wasan da zasu wakilci wannan kungiya, ba abinda nake jira face na fara taka leda a wannan kungiya" a cewar Musa.

Amma magoya baya da dama na ganin hakan a matsayin koma baya ne ga harkar kwallon kafarsa. Wasu na ganin cewa ba’a yanzu ya kamata ace ya bar nahiyar turai da taka leda ba, domin a cewarsu yana bukatar ya kafa tarihi musamman a gasar Premier ta kasar England.

Musamman yanayin taka ledarsa zai iya samun matsala ta ci baya domin zai fi kyau yana buga wasa a nahiyar turai kamar irin su England, Spain ko kasar Italy don yana zai dinga haduwa da manyan ‘yan wasan Duniya wanda zasu ke yin gogayya kuma hakan zai taimaka wajen cigaban kwallonsa.

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Ra'ayi riga: Anya kuwa Ahmed Musa komawarsa cikin Larabawa da taka leda ba gwari yayi ba?

Wasu kuma na ganin cewa yayi abinda ya kamata, wato dai duk dodo-daya ake wa tsafi. Abin nufi a nan shi ne masu ra'ayin goya masa baya suna ganin cewa lamarin duk na neman kudi ne, don haka dan wasan yayi abinda ya dace saboda a can cikim Larabawan ne zai samu kudade masu tarin yawa fiye da wanda yake samu a Nahiyar turai.

Kurunkus wai an yiwa mai zani daya sata, Ahmed Musa dai ya zama dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr kuma zamu cigaba da biyayyarsa domin ganin wani irin gudunmawa zai bawa wannan sabuwar kungiya tasa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel