Shehu Sani a neman kariyar Allah daga sharrin masharranta da hassadan mahassada

Shehu Sani a neman kariyar Allah daga sharrin masharranta da hassadan mahassada

Wakilin jama’an Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ba za fita daga cikin jam’iyyar APC ba, don haka magauta sai su san nayi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Shehu Sani ya bayyana haka ne da safiyar Laraba, 1 ga watan Agusta, a shafinda na kafar sadarwar zamia ta Facebook, inda yake jaddada ma al’ummar Kaduna ta tsakiya cewa ana mugun tare, tare da jan hankalin mahassada.

KU KARANTA: Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri

“Jamma'an Kaduna ta tsakiya ina kara jaddada maku cewa ana matukar tare.Babu maganan chanza sheka.Abin da kuke so shi nake so.Akidar mu ta talakawa ne. Inda talakawa suka ce inbi nan zanbi.Muna tare jiya,muna tare yau,Muna tare Kullum Insha Allah.” Inji Sanatan.

Sani ya cigaba da yin kira ga duk ma mahassa ko bakin ciki da kuma haddasa rikici don bata masa suna saboda matsayin da Allah ya bashi ko kuma don dangantaka da zumuncin dake tsakaninsa da talaka, inda yace mutum ma zai yi ne ya bari.

Sanata ya kara da cewa: “Mai kokarin ya fidda mu Jammiyan APC ya ma daina Dan ba zai iya ba.Abin da Allah ya shuka ya kuma tsare lallai sai dai asa masa ido, abu daga Allah sai kallo.”

Daga karshe Sanatan ya tabbatar da cewa Allah ne ka bada mulki ga duk wana yaso, ba wani muhaluki ba, don haka yayi rokon Allah kare shi daga sharrin masharranta da hassadan mahaddasa, da kuma bakin cikin masu bakinci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel