Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa saboda ta hana shi N20,000
Wani matashi mai shekaru 27, Emmanuel Eghaghe, ya tattara komatsan sa ya gudu bayan ya yiwa mahaifiyarsa duka har sai da ta mutu saboda wai ta hana shi kudin kashe N20,000.
Rahotanni sunce Emmanuel ya tafi shagon mahaifiyarsa mai shelkaru 61 ne a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2018 a layin Jinadu da ke Ajangbadi a jihar Legas.
Saturday Punch ta ruwaito cewa Emmanuel ya shaida a mahaifiyarsa Helen cewa yana bukatar kudin kashewa har N20,000 sai dai daga bisani ya fara bugunta bayan taki bashi kudin a kokarinsa na karbar kudin a dole.
DUBA WANNAN: Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari
Mahaifiyar ta samu rauni a kanta sakamakon buga kanta da ya yi da bango inda jini ya rika kwarara. Hakan yasa Emmanuel ya cika wandonsa da iska ya bace har yanzo ba'a gano inda yake ba.
Wani makwabcin Helen da ya bukaci a sakayya sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa an shigar da kara ofishin yan sanda dake Ajangbadi an kuma sanar da dan uwar mahaifiyar dake Benin cewa Helen ta rasu.
Majiyar ta kuma ce 'yar uwar wanda ake tuhuma da kisar tana da Otel a unguwar inda ta bawa mahaifiyarsu daki guda don ta rika zama kuma ita ne ta bude mata shago a gaban Otel din don ta rika samun kwabo da sisi.
Kakakin yan sandan jihar Legas, CSP Chike Oti, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa jami'an hukuman sun bazama don nemo wanda ake tuhuma da aikata wannnan mummuna ta'asa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng