Ba kanta: Gwamnan Nasir El-Rufai ya tsine wa sanatocin Kaduna
Yanzu haka dai wasu kalamai da ke nade a faifan sauti masu yawo a tsakanin al'umma da wasu ke wa kallon na ingiza jama'a ne su dauki doka a hannunsu, mun samu cewa gwamnan jihar Kaduna, ya bukaci al'ummar jihar Kaduna da su dauki matakai kan sanatocin da suka fito daga jihar.
Kamar yadda muka ji a muryar gwamnan, Nasir Ahmad El-Rufai ya ce "wadannan dattijan (sanatocin Kaduna) banza ne domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar."
KU KARANTA: Jonathan ne ya lalata harkar lafiya a Najeriya - Buhari
Legit.ng ta samu cewa haka zalika kuma ya yi kira ga dukkan magoya bayan sa da su fito kwansu da kwarkwatar su su tunkari Sanatocin domin a cewarsa "ba sa kaunar jihar."
Sanatocin da Gwamnan ya ke nuni izuwa gare su sun hada da Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma Laah wadanda yace sun hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng