Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuka 16 da dimbin dukiya ta N70m

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuka 16 da dimbin dukiya ta N70m

- Hukumar kashe gobara na jihar Kano tayi nasarar ceto rayyuka 16 tare da dimbin dukiya na naira miliyan 70 cikin watan Afrilu

- Hukumar tace mafi yawancin gobaran sun faru ne saboda amfani da kayan wuta marasa nagarta tare da sakaci wajen amfani da kaya masu amfani da lantarki

- Hukumar ta shawarci al'umma su guji ajiye man fetur da wasu abubuwan da masu kama da fetur din a gidajensu saboda kare afkuwar gobara

A yau Juma'a ne Hukumar kashe gobara na jihar Kano ta bayar da sanarwar cewa ta samu nasarar ceto rayyuka 16 da kuma dukiyoyi wanda kudin su ya kai N70m daga gobara 86 da shida da suka faru a jihar cikin watan Afrilu.

Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed yayin wata hira da yayi da kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) a birnin Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuka 16 da dimbin dukiya ta N70m
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuka 16 da dimbin dukiya ta N70m

Kazalika, Mohammed kuma ya ce an rasa rayyuka guda 15 tare da gidaje 65 da shaguna 21 da gobarar ta lalata.

KU KARANTA: Hukumar INEC tace makafi zasu kada kuri'a ta hanyar amfani na'urar Braille

Ya cigaba da cewa darajar kadarorin da aka rasa ya kai kimanin naira miliyan 13 inda hukumar ta samu kiran neman taimako guda 13 da kuma wasu kiran amma na bogi guda 21 duk a cikin watan na Afrilu.

Mai magana da yawun hukumar kara da cewa akasarin gobara sun faru ne sanadiyar rashin amfani da wayoyi masu inganci wajen janyo wutan lantarki cikin gidaje, amfani da na'urar taasa ruwa (boiling ring), hatsari da kuma rashin iya amfani da kayan wuta da resho mai amfani da iskar gas.

Daga karshe, ya shawarci mutane suyi taka tsan-tsan wajen amfani da wuta kuma su guji ajiye man fetur da wasu abubuwan da masu kama da fetur din a gidajensu saboda kare afkuwar gobara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel