Yadda wasu daliban Fimari su 6 suka tsallake rijiya da baya yayin da suka afka cikin Masai
Wasu yara kanana su shidda, dake karatu a wani Firamari dake yankin Nakuru a babban birnin kasar Kenya, Nairoibi, sun sha da kyar bayan da wani shadda ya rufta dasu, inda baraguzan shaddan suka daddannesu, kamar yadda rediyon BBC Hausa ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba da wani kauyen yankin Nakuru, kuma lamarin ya samo asali ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka sha kamar da bakin kwarya a yankin.
KU KARANTA: Yan bangan siyasa sun kai ma wani na hannun daman gwamnan jihar Kebbi farmaki
Karfin wannan ruwa ne ya sanya masan zurmawa, sai dai a wannan lokaci daliban na kusa da shaddar, wanda haka yayi sanadiyyar jikkatar guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran hudu suka sha ba tare da samun ko kwarzane ba.
A kokarin ceto daliban daga halin da suka shiga, sai da aka hada karfi da karfe tare da iyayensu, Malaman makarantar da jami’an aikin ceto, inda suka tono baraguzan shaddar, suka zakulo daliban daya bayan daya.
Rahotanni sun tabbatar da a yan kwanakin nan ana yawan samun saukar mamakon ruwan sama a kasar Kenya, wanda hakan ke janyo ambaliyar ruwa ko wata matsala makamanciyar haka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng