Da lukuti: Hotunan daya daga cikin jarirai mafi nauyi a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6

Da lukuti: Hotunan daya daga cikin jarirai mafi nauyi a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6

- Hotunan daya daga cikin jarirai mafi nauyi a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6

- Matar sunan ta Helen Chepkwemoi Kesis yar kauyen Kaptama duk dai na kasar ta Kenya

- Yanzu haka uwar da jaririyar ta suna kwance ne a asibiti suna kara murmurewa

Malaman asibiti da masu karbar haihuwa a wata asibitin garin Bungoma County sun shiga al'ajabi biyo bayan wata mata da ta haifi daya daga cikin jarirai mafiya girma a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6.

Da lukuti: Hotunan daya daga cikin jarirai mafi nauyi a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6

Da lukuti: Hotunan daya daga cikin jarirai mafi nauyi a duniya mai nauyin ma'aunin kilogiram 6

KU KARANTA: Buhari ba zai samu tikitin tazarce kai tsaye ba - APC

Ita dai matar mai suna Helen Chepkwemoi Kesis yar kauyen Kaptama duk dai na kasar ta Kenya ta haifi jaririyar ta ta ne a ranar Alhamis din da ta gabata kuma har ma ta saka mata suna Blessing Cherotich.

Legit.ng ta samu cewa matar dai daman tana da tarihin haihuwar yara masu kiba inda duka manyan 'ya'yan na ta su kusan 3 duk da girman gaske aka haife su duk kuwa da cewa ta haife su ne ba tare da aikin tiyata ba.

Yanzu haka dai kamar yadda muka samu, uwar da jaririyar ta suna kwance ne a asibiti suna jinya tare da kara murmurewa kafin a sallame su su tafi gida.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel