Wata mai ciki ta maka mijinta a kotu saboda ya kauracewa saduwa da ita
Wata mata, Lauratu Abdullahi; mai shekaru 30, ta bukaci kotun shari'ar Musulunci dake magajin gari a Kaduna ta raba aurenta da mijinta saboda ya daina saduwa da ita tun bayan da cikinta ya girma.
Lauratu, ta shaidawa kotu cewar, mijinta, Yahaya Tanko, na yawan cin zarafinta duk da baya iya biyan bukatunta.
Ta sanar da kotun cewar mijinnata ya barta da yunwar abinci da kuma ta jima'i har na tsawon watanni hudu.
Lauratu, uwar 'ya'ya biyar, ta ce, "Ina son kotu ta raba aurenmu saboda a bayyane take cewar mijina baya so na kuma bai damu da ni ba a halin yanzu."
Saidai, mijinta, Tanko, ya musanta dukkan zargin da take yi masa tare da shaidawa kotu cewar har yanzu yana son matar sa, sannan ya kara da cewar, matar ta shi na dauke da cikin wata hudu.
"Ina son kotu ta shaida cewar, batun bana saduwa da mata ta, ba gaskiya bane domin ko a yanzu tana dauke da cikin wata hudu," a cewar Tanko.
DUBA WANNAN: Kudirin gyaran dokar zabe: Majalisar jihar Kano tayi taron gangamin nuna goyon baya ga Buhari
Alkalin kotun, Malam Musa Sa'ad, ya tambayi Lauratu, ko da gaske tana dauke da juna biyu, sai ta amsa da cewar hakane tare da shaida masa cewar cikin ya shiga ne tun watan farko da suka kwanta tare da Tanko.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an daga sauraron karar ya zuwa ranar 3 ga watan Afrilu domin ma'auratan su zo da wakilai ko iyayensu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng