Cikin sanatoci ya duri ruwa: Jama’an mazabunmu sun kosa mu koma gida su yi mana rubdugu game da canza tsarin zabe – Sanata Ali Wakil

Cikin sanatoci ya duri ruwa: Jama’an mazabunmu sun kosa mu koma gida su yi mana rubdugu game da canza tsarin zabe – Sanata Ali Wakil

Sanatan al’ummar Bauchi ta kudu, Sanata Ali Wakil ya shaida cewa al’ummar jihar Bauchi sun shirya tsaf don yi ma sanatocinsu guda uku da suka fito daga jihar rubdugu sakamakon amincewa da suka yi da kudurin sauya jerin gudanar da zabuka.

Sanata Ali Wakili ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Post a garin Abuja, inda yace jama’a na ganin kamar majalisar ta amince da wannan kudiri ne don ta zama matsala ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk kuwa da cewa shi bai amince da kudurin ba.

KU KARANTA: Babban lauyan gwamnati ya shawarci Buhari ya dakatar da EFCC daga binciken tsohuwar minista Diezani Allison da Bello Adoke

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ali yana cewa jita jita na yaduwa a jihar Bauchi cewar suna daga cikin sanatocin dake shirya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kullalliya don ya fadi zabe a shekarar 2019.

Cikin sanatoci ya duri ruwa: Jama’an mazabunmu sun kosa mu koma gida su yi mana rubdugu game da canza tsarin zabe – Sanata Ali Wakil
Sanata Ali Wakil

Sai dai Sanatan ya musanta zargin da ake yi na cewa wai Sanatoci na shiga inuwar Buhari suna cin zabe, inda yace Allah ne mai bada mukami, ya kara da tabbatar da cewa Buhari na da dimbin masoya a jihar Bauchi.

Sanata Ali yace a gaskiya jama’an Bauchi ta kudu basu amince da kudirn sauya jerin zabe ba, don haka ne ya say a nuna rashin amincewarsa da wannan kudiri tun a majalisar dattawa.

Idan za'a tuna majalisun dokokin Najeriya sun kammala aiki kan wani kudiri dek jiran sa hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai raba zaben shugaban kasa da yan majalisu, inda za'a mayar da zaben shugaban kasa zuwa karshe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng