An samu wani tsoho a Najeriya mai shekaru 145 a duniya, ga hotunansa
Wani Fasto a Najeriya, Ikenna Ofodile, ya watsa hotunansa da wani tsoho mai shekaru 145 a duniya da ya ce kakansa ne.
Hoton Faston da dattijon ya jawo hankalin jama'a da dama a dandalin sada zumunta na Facebook, inda jama'a ke yin tambayoyi daban-daban a kan tsohon.
Bayan hotunan tsohon, fasto Ikenna ya nuna hoton wata dattijuwa matar tsohon, saidai bai ambaci ko shekarunta nawa a duniya ba.
Wasu na son sanin ko tsohon yana iya magana ko yana gani da idonsa. Yayin da wasu kuma ke ruwan addu'o'i ga tsohon.
Mai yiwuwa, a halin yanzu, babu mutumin da ya fi wannan tsoho shekaru a Najeriya domin ko a duniya ma, samun sa'anninsa sai an tona.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng