Najeriya ta zo na biyu a jerin kasashen duniya mafi rashin wutan lantarki a 2017

Najeriya ta zo na biyu a jerin kasashen duniya mafi rashin wutan lantarki a 2017

- Najeriya na cikin jerin kasashe mafi talaucin lantarki a duniya

- Duk da karin farashin wutar lantarki, yan Najeriya ba su samun wuta yadda aya kamata

Najeriya ta zo na biyu a jerin kasashen duniya mafi rashin wutan lantarki yayinda karfin wutan lantarki ya sauko 3,851 megawatts, MW.

Lissafin Spectator Index na lalatan wutan lantarki a 2017, ya bayyana cewa a wannnan sabon rahoto da ta saki a jiya, kasashe 137 da aka gudanar da bincike a kai, kasar Yemen ce ta zo kasa na daya mafi rashin ingancin wutan lantarki sai kuma Najeriya.

Sauran kasashen sune kasar Haiti, Lebanon da Malawi.

Najeriya ta zo na biyu a jerin kasashen duniya mafi rashin wutan lantarki a 2017
Najeriya ta zo na biyu a jerin kasashen duniya mafi rashin wutan lantarki a 2017

Kasar Ethiopia ce ta zo na 37, kasar Afrika ta kudu na 41, kasar Aljeriya na 45.

Rahoton ya bayyana cewa matsakaicin wutan lantarkin da kamfanonin samun wuta suka rabawa jama'a Migawat 3, 851.06mw, wanda ke nuna cewa ya rage da 168.58mw.

KU KARANTA: An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

Binciken ya nuna cewa an samu nuksani wajen samun wutan ne saboda isasshen iskar gas wanda za'ayi amfani da shi wajen samar da wutan.

Bangaren wutan lantarki ta yi asaran N1,121,000,000 a jiya kadai 14 ga watan Junairu 2018, saboda rashin isasshen Gas, kayan aiki, da kuma ruwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ko Ku same mu a:

https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng