An tuhumi wasu matasa 2 da laifin killace matar aure da lalata a garin Zariya

An tuhumi wasu matasa 2 da laifin killace matar aure da lalata a garin Zariya

Wata babbar kotun shari'ar musulunci dake zamanta a unguwar Tudun Wada Zariya ta bayar da umurnin daure wasu matasa 2 a gidan yari bisa tuhumar su da laifin hada baki tare da boye wata matar aure da kuma yin lalata da ita har na tsawon kwanaki biyar.

Dan sanda mai gabatar da kara dai Sajen Adamu yahaya ne ya gabatar da wadanda ake zargin Usman Yusuf da Rabi'u Muhammadu a gaban kotun inda ya yace sun aikata laifin ne a kwanan baya.

An tuhumi wasu matasa 2 da laifin killace matar aure da lalata a garin Zariya
An tuhumi wasu matasa 2 da laifin killace matar aure da lalata a garin Zariya

KU KARANTA: Za'a fara anfani da adai-daita mai anfani da haske rana a Najeriya

Legit.ng dai ta samu cewa wadanda ake tuhumar na farko Usman Yusuf ya ansa laifin sa na yin lalata da matar yayin da dayan kuma Rabi'u Muhammad yace shi bai ma san tana da aure ba kuma bai yi lalatar da ita ba.

Daga nan ne dai sai alkalin kotun mai suna Aminu Sa'ad ya umurci a tura matasan biyu a gidan yari har sai nan da sati biyu masu zuwa domin a kammala bincike.

Da take tofa albarkacin bakinta, matar mai suna Amira Usman ta bayyana cewa mijin ta ne ya bata mata rai ita kuma sai ta fito ta bar masa gidan sa ta kuma tafi dakin samarin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng