Za’a saki fim din Abu Hassan a cikin wannan watan

Za’a saki fim din Abu Hassan a cikin wannan watan

Rahotanni sun kawo cewa shahararren fim din nan da mutane ke ta simayin fitowar sa wato Abu Hassan na kan hanya.

Za’a kaddamar da wasan a gidan kallo sinima a ranar 27 ga watan Oktoba a jihar Kano.

Jarumin da ya dauki nauyin shirya fim din, Zaharaddeen Sani ne ya sanar da hakan ga jaridara Premium Times harma yace tuni sun kammala shirya fim din.

A cewar sa zasu fara gabatar da shi a gidan kallon Queen House Sinima dake Ado Bayero Mall dake jihar Kano, sannan daga bisani su haska shi a sauran jihohin kasar.

Za’a saki fim din Abu Hassan a cikin wannan watan
Za’a saki fim din Abu Hassan a cikin wannan watan

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya ba wata nakasasshiya kyautar naira miliyan 1 (hotuna)

Jarumin ya kuma ce a ranar da za’a fara haska fim din, za’a ga jaruman da suka fito a fim din ido da ido.

Abu Hassan dai fim ne da ya bada labarin ta’addanci. Zaharaddeen ya ce ya shirya fim din ne domin ya nuna illar wannan abu da irin kalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta wajen yakar shi, da kuma yadda iyaye za su kula da ‘yayan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng