An soke rajistar wata Jaridar ‘Yan Shi’a

An soke rajistar wata Jaridar ‘Yan Shi’a

– Kungiyar ‘Yan Jarida na Kasa ta soke rajistar Jaridar Al-Mizan

– NUJ tace tayi kuskure wajen rajistar Jaridar

– Jaridar Al-Mizan ta ‘Yan Shi’a ce

An soke rajistar wata Jaridar ‘Yan Shi’a
An soke rajistar wata Jaridar ‘Yan Shi’a

Kungiyar NUJ ta ‘Yan Jaridun Najeriya ta soke rajistar Jaridar nan ta Al-Mizan. Wannan mataki dai ya zo ba da bata wani lokaci ba kamar yadda Kungiyar ta bayyana bayan wani taron da tayi a karshen makon da ya wuce.

Sakataren Bangaren Kungiyar na Jihar Kaduna, Dauda Idris Doka ya sa hannu wajen matakin da aka dauka. Kungiyar ta bayyana cewa ta gano Jaridar ta ‘Yan Shi’a ce a zaman ta da tayi na zartarwa a ranar 29 ga watan nan.

KU KARANTA: An kai hari Kasar Saudiyya

Kungiyar ta NUJ dai tace ba ruwan ta da wani addini, asali ma dai tana kokarin kare duk wasu Addinai da kuma Kabilu na Kasar ne. Kungiyar don haka tace tayi kusukuren ba Jaridar Al-Mizan lasisi a baya. Daga yanzu dai bai hallata Jaridar ta ci gaba da aiki ba.

Jaridar Al-Mizan din da kuma ta Turancin ta watau Pointer Express ta Kungiyar IMN ce ta Shi’a. A bay dai NUJ ta hana Jaridu da dama lasisi saboda wannan dalilai.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng