Alamomin ciwon Sankarar Huhu
- Ya na da kyau mu sani cewa, wayewar dan Adam na kara habaka cikin sauri har ta kai an samo maganin cututtuka da dama wadanda shekaru 50 da su ka wuce babu maganinsu.
- Amma abin takaici da bakin ciki, kansa ko kuma ciwon sankara na daya daga cikin matsalolin da a ka rasa yadda za a magance su. Har yanzu ba wani magani da zai taimaka wajen yakar cutar.
Al'amarin wannan cuta sankarara Huhu na kara girmama da sauri duk shekara, da yawa daga likitoci sun yi bayanin cewa, cutar na afkuwa ne bisa dalilai na tsufa saboda ta fi kama tsofaffi.
Ta wajen kisa kuwa, cutar na matsayi na uku a duniya. Daya daga cikin ire-iren cutar sankara da suka fi yaduwa ita ce kansar ko cutar Sankarar huhu.
KU KARANTA KUMA: Rikicin Kaduna: El-Rufai ya na abin da ya kamata –Adesina
Alamomin ciwon sankarar huhu ka iya bayyana ta hanyoyi daban-daban, Wannan kuwa na tasirantuwa ne da wajen da cutar ta ke, da kuma matakin da ta ke, Yawanci ba a gano cutar da ke da alaka da gyambo a matakin farko.
Alamomin ka iya zama kamar na sauran cututtuka wadanda ba a cika damuwa da su ba. Kebantattun alamomin kansar hunhu su na bayyana ne a matakin karshe na cutar. A wannan makala, za mu kalli alamomin cutar wadanda za su bukaci kulawa ta gaggawa.
Kansar da ba a gane alamunta ka iya faruwa a farko- farkon cutar. Wanda gano ta abu ne mai sauki a wannan lokacin indai akwai damar yin hoton kirji. Kamar yadda kididdiga ta nuna, kashi 25 na masu cutar ba sa iya gano dan karamin gyambo bayan bin wannan hanyar.
Gaba dayan alamomin cutar kansar hunhu na iya rabuwa gida uku:
1. Alamomin da ke da jibi da fadadar bututun da ke kai wa huhu iska :
- Yawan tari
- Ciwon kirji
- Tarin jini
- Kaki da toshewar numfashi
2. Alamomin da ke nuni da fitowar sabon gyambo a gabobin da ke kusa:
- Cushewar abinci a bututun da ke daukar abinci daga baki zuwa ciki
- Kumburin fuska da wuya
- Radadi a hannu da kafada a wajen da ciwon ya shafa
- Dashewar murya
- Kumburin jiki daga sama da sauransu.
3. Alamomin da ke da alaka da maye:
- Alamomin gyambo
- Kasala, gajiya, kasa yin aiki, rashin cin abinci, rama,
- Jin sanyi, zufa, zazzabi da tari.
- Fitowar gyambo a wuya da hammata da dai sauransu.
Yanda za a magance kansar Huhu.
Cin nasarar maganinta ya dogara ne kai tsaye ga matakin da ta ke. Me ya sa likitoci su ka bada shawarar a dinga yin hoton huhu a kai a kai, wanda zai taimaka wajen gano gyambo ko da kuwa a matakin farko ne?
Idan a ka gano mutum na dauke da kansar huhu. Hakan na nufin gyambon ya yaryadu zuwa gabobin da ke kusa, kuma ba za a iya magance shi ba. A irin wannan, abin da kawai likitoci za su iya yi shi ne kula da rayuwar mai cutar, da kuma rage masa radadinta ta hanyar amfani da magungunan rage radadi, da sauransu.
Mafi yawancin mutanen da a ka samu nasarar yi musu magani suna dawowa su yi rayuwa kamar yadda su ka saba. Ya kamata a sani cewa, Idan kana zargin wani naka na dauke da wannan cutar, to ka yi kokarin neman taimako a asibitin da ke kusa da kai.
Asali: Legit.ng