Lionel Messi Ya Zarce Ronaldo, Suárez, Ya Kafa Sabon Tarihi a Buga Kwallon Kafa

Lionel Messi Ya Zarce Ronaldo, Suárez, Ya Kafa Sabon Tarihi a Buga Kwallon Kafa

  • Lionel Messi ya karya tarihin duniya bayan ya zama dan wasan da ya fi kowa yawan ba da kwallayen da ake zurawa a raga
  • Ba da kwallon da ya yi a wasan Inter Miami da New York City da suka lallasa su 5–1 a kofin MLS Cup ya sa Messi ya kafa tarihi
  • Shahararren dan kwallon mai shekaru 38 yanzu yana da jimillar kwallaye 896, kuma ya ba da kwallaye 405 da aka zura su a raga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Lionel Messi ya kafa sabon tarihin kwallon kafa sakamakon zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan ba da kwallon da aka zura a raga.

Shahararren ɗan wasan Argentina ya ba da kwallaye 405 da aka zura a raga yayin da Inter Miami ta lallasa New York City da ci 5–1 a wasan ƙarshe na cin kofin kofin MLS.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya karbi mutane da 'dan bindiga ya saki bayan sulhu a Katsina

Messi ya zama dan wasa mafi yawan kwallayen da ya ba da aka zura a raga.
Lionel Messi yana rike da kofin MLS bayan Inter Miami ta lallasa New York City da ci 5-1. Hoto: @FOXSoccer
Source: Twitter

Messi ya kafa tarihi a kwallon kafa

Messi ya ba Mateo Silvetti kwallon da ya ci a minti na 67, abin da ya sa ya zarce Ferenc Puskás wanda ya ke da kwallaye 404 da ya ba da aka ci, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin wannan wasa, Messi da Puskás suna kunnen doki a yawan kwallayen da suka ba da aka ci, watau 404.

Sai dai a wannan wasan na karshe, kwallon da Messi ya ba da aka ci ta sa ya zarce shahararrun ‘yan wasa kamar Pelé, Johan Cruyff da Thomas Müller.

Ga jerin sababbin manyan 'yan wasa da suka fi yawan ba da kwallayen da aka ci a tarihi:

  1. Lionel Messi – 405
  2. Ferenc Puskás – 404
  3. Pelé – 369
  4. Johan Cruyff – 358
  5. Thomas Müller – 352
  6. Luis Suárez – 317
  7. Kevin De Bruyne – 316
  8. Ángel Di María – 313
  9. Cristiano Ronaldo – 304
  10. Luís Figo – 283

Kara karanta wannan

Shugaban kasar da Trump ke son cafkewa ya fito kan titi, ya fada wa Amurka ko gezau

Yawan kwallayen Messi a tarihi

A yau Messi yana da tarihin gudummawar cin kwallo mafi girma a duniya. Ya ci kwallaye 896 a rayuwar taka ledasa sannan ya ba da tallafin kwallaye 405, in ji rahoton Sport Ratio.

A wasansa na baya-bayan nan da Inter Miami, ya koma kan jerin shahararrun ‘yan wasa da suka fi nasarori a tarihin ƙwallon kafa.

Lionel Messi ya tattara gagarumin tarihi a duniyar kwallon kafa. Ya lashe Ballon d’Or guda 8, mafi yawa a tarihin wasan, sannan ya lashe kambun dan wasa mafi soyuwa ga FIFA sau uku.

Harilayau, Messi ya rike tarihin cin kwallaye mafi yawa a La Liga (474), Supercopa de España (14), da UEFA Super Cup (3).

Messi yanzu ya na da yawan kwallaye 405 da ya ba da aka ci, sanna ya zura kwallaye 896 a raga.
Kungiyar kwallon kafar Inter Miami ta na murnar lashe kofin MLS bayan doke New York City da ci 5-1. Hoto: @InterMiamiCF
Source: Getty Images

Yawan kofunan da Messi ya daga a tarihi

Messi ya daga kofuna 47 a kungiyoyin kwallon kafa da kuma kasarsa Argentina:

  • 35 tare da Barcelona
  • 3 tare da PSG
  • 3 tare da Inter Miami
  • 6 tare da Argentina

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

Bayan Inter Miami ta lashe kofin MLS Eastern Conference, Messi ya kai tarihi na lashe kofuna 47, wanda ya zama mafi yawa da kowanne ɗan wasa a duniya.

An fara maganar komawar Messi Saudiyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Lionel Messi na iya komawa Saudiyya taka leda bayan bude tattaunawa tsakanin wakilansa da masu harkokin wasanni.

Dan wasan ya bayyana cewa tun da farko ya yi tunanin zuwa Saudiyya kafin ya yanke shawarar komawa Inter Miami a Amurka.

Zuwa yanzu ba a kammala wata yarjejeniya ba, amma yana iya komawa wata kungiya a Saudiyyabayan karewar kwantiraginsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com