Jerin duka ‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi yawan kwallaye a gida

Jerin duka ‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi yawan kwallaye a gida

Da kwallayensa biyu a wasan Portugal da kasar Sweeden, Cristiano Ronaldo ya sake samun matsayi a sahun ‘yan kwallon da su ka ci wa kasarsu kwallaye mafi yawa.

Duk Duniya, mutum daya ne ya taba cin kwallaye 100 a gida bayan Ronaldo, wannan kuwa shi ne Ali Daei. Daei ya bugawa Iran wasanni 146 kafin ya yi ritaya da kwallon kafa.

Ga jerin ‘yan wasa 10 da ke kan gaba a adadin kwallayen da su ka zura a gida:

1. Ali Daei

Ali Daei shi ne kan gaba a wannan jeri da kwallaye 109 wadanda ya ci tsakanin 1993 zuwa shekarar 2006.

2. Cristiano Ronaldo

A ranar Talata, Ronaldo ya shiga maki uku, ya ci kwallayensa na 100 da 101. Saura kwallaye takwas ya kamo Daei.

KU KARANTA: Ronaldo ya nuna bajinta, ya zura kwallo na 100 a Portugal

3. Ferenc Puskas

Na uku shi ne Ferenc Puskas na Faransa wanda ya ke da kwallaye 84. Tsohon ‘dan wasan na Real Madrid ya yi tashe a da.

4. Godfrey Chitalu

‘Dan wasan Afrika da ya shiga wannan sahu shi ne Chitalu wanda ya zurawa Zambiya kwallaye 79 a lokacin da ya ke wasa.

5. Hussein Saeed

Kafin ya yi ritaya, sai da Hussein Saeed ya ci kwallaye 78 da rigar kasar Iraki tsakanin 1970s zuwa shekarun 1980s.

6. Pele

Duk yawan kwallayen Pele a Duniya, idan ana maganar kwallayen da aka ci wa kasa shi ne na 6 da kwallaye 77 a Brazil.

7. ‘Yan wasa 3

‘Yan kwallo uku aka samu sun ci wa kasarsu kwallaye 75 – Su ne: Sandor Kocsis (Hungary), Kunishige Kamamoto (Jafan), da Bashar Abdullah (Kuwait).

KU KARANTA: Suarez zai tashi daga Barcelona, Messi ya na nan daram-dam-dam

Jerin duka ‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi yawan kwallaye a gida
Pele Hoto: Britannica
Asali: Twitter

8. Sunil Chhetri

Sunil Chhetri shi ne na 8 a jerin kamar yadda Givemesport ta rahoto, ya na da kwallaye 72. Har yau ya na bugawa Indiya.

9. ‘Yan wasa 4

‘Yan wasan da su ka ci wa kasarsu kwallaye 71 su ne: Miroslav Klose, Kinnah Phiri, Majed Abdullah, da Kiatisuk Senamuang na Jamus, Malawi da Saudi da kasar Thailand.

10. ‘Yan wasa 4

Akwai ‘yan wasa hudu da su ka taba cin kwallaye 70 a gida, daga ciki har da Lionel Messi na Argentina. Sauran su ne Piyapong Pue-on, Stern John da Hossam Hassan.

Sauran shararrun ‘yan wasa da su ke da kwallaye da-dama amma ba su samu shiga sahun farko ba sun hada da Didier Drogba, Robbie Keane, Neymar Jr., Zlatan Ibramovich da Ronaldo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng