Super Eagles: Lokuta 6 da Najeriya ta Fafata a Gasar Kofin Duniya a Tarihi
Legit Hausa ta hada muku rahoto na musamman game da lokuta shida da Najeriya ta samu damar zuwa gasar kofin duniya a tarihi.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A jiya Lahadi kasar DR Congo ta doke Najeriya a wasan neman shiga gasar kofin duniya na 2026.
Faduwa a wasan ya sanya Najeriya rashin samun damar buga gasar kofin duniya karo na biyu a jere.

Source: Getty Images
A wannan labarin, mun hada muku rahoto na musamman a kan lokuta shida da Najeriya ta fafata a gasar a tarihi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Najeriya ta fara buga kofin duniya a 1994
Najeriya ta shiga rukunin D a gasar kofin duniya ta FIFA na 1994 da aka yi a Amurka, wanda shi ne karon farko da Super Eagles ta buga.

Kara karanta wannan
'Congo ta yi tsafi ta fitar da Najeriya a neman gurbin kofin duniya,' Kocin Super Eagles
An buga wasan farko a ranar 21, Yuni, 1994, sannan aka buga wasan karshe a ranar 30, Yuni, 1994.
Shafin National Football Teams ya wallafa cewa kasashen da ke rukunin D sun kunshi Argentina, Greece, Najeriya da Bulgaria.
Najeriya ce ta yi nasara a rukunin bisa yawan kwallayen da ta zura; Bulgaria ta zo ta biyu, sannan Argentina ta zo ta uku.

Source: Getty Images
Bincike ya nuna cewa kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta kammala gasar kofin duniya ta 1994 a matsayi na tara.
Kocin Najeriya na lokacin shi ne Clemens Wester, Kyaftin din kungiyar Super Eagles kuma shi ne Stephen Keshi.
’Yan wasan da suka taka rawa sun hada da Rashidi Yekini, Jay-Jay Okocha, Finidi George, Daniel Amokachi, Sunday Oliseh, Emmanuel Amunike.
Najeriya ta hango nasara a kan Italiya, amma lamari ya canza a mintunan karshe, Roberto Baggio ya zura kwallaye biyu, aka koro kasar Afrikar gida.
2. Najeriya ta buga gasar kofin duniya a 1998
Najeriya ta sake samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 1998 bayan shiga gasar a karon farko a shekarar 1994.
A lokacin, an nada Bora Milutinović dan asalin Serbia a matsayin koci, bayan an sallami Philippe Troussier makonni kadan kafin fara gasar.
BBC ta ce tawagar ta kunshi Jay-Jay Okocha, Sunday Oliseh, Finidi George, Nwankwo Kanu, Victor Ikpeba, Tijjani Babangida, Daniel Amokachi, Celestine Babayaro da Taribo West.

Source: Getty Images
Super Eagles ta buga wasanni da Spain, Bulgaria da Paraguay a rukuni na farko yayin da aka yi gasar a kasar Faransa.
Duk da kyakkyawan farawa da rawa mai kyau, Najeriya ta yi rashin sa’a inda aka fitar da ita a zagaye na 16 da Denmark ta doke ta da ci 1-4.
3. Najeriya ta koma kofin duniya a 2002
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta fuskanci mummunan karshe a gasar cin kofin duniya ta 2002, inda ta kare a matsayi na ƙarshe a Rukuni F.
Rukunin ya kunshi manyan ƙasashe uku bayan Najeriya: Argentina, England da Sweden, wadanda suka shahara wajen gogewa a matakin duniya.
Daga cikin fitattun ‘yan wasan akwai Julius Aghahowa, wanda ya kasance muhimmin tauraro a tawagar.

Source: Getty Images
4. Najeriya ta fafata a Afrika ta Kudu a 2010
Super Eagles ta Najeriya ta sake samun damar shiga gasar kofin duniya a gasar da aka yi a kasar Afrika ta Kudu a 2010.
Karkashin jagorancin kocin Sweden, Lars Lagerbäck, Najeriya ta samu maki 1 kacal cikin wasanni uku, ta kuma kare a matsayin na uku a rukuni.
Wannan sakamakon ya sanya Super Eagles ta kammala gasar a matsayi ta 27 daga cikin ƙasashe 32 da suka halarta.

Source: Getty Images
Hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce mai zafi a gida, inda shugaban ƙasa a wancan lokacin, Goodluck Jonathan, ya ayyana dakatar da ƙungiyar na tsawon shekara biyu.
Al-Jazeera ta rahoto cewa daga baya Jonathan ya sauya matsaya daga matakin bayan rokon da wasu 'yan kasa suka yi.
5. Najeriya ta shiga gasar kofin duniya a 2014
Najeriya ta sake samun damar shiga gasar kofin duniya a 2014 da aka yi a kasar Brazil, inda ta dan taka rawa.
Kasar Faransa ta kawar da Super Eagles daga gasar, inda suka kammala a matsayi na 16 a shekarar.
Kungiyar ta kasance a ƙarƙashin jagorancin Stephen Keshi, wanda shi kaɗai ne ɗan Najeriya da ya taka leda a matsayin kyaftin kuma daga baya ya horar da ƙasar a gasar Duniya.

Source: Getty Images
Super Eagles sun fafata da Iran, Bosnia da Argentina a rukuni, inda suka nuna ƙarfin hali da tsayayyen tsarin wasa.
Daga cikin fitattun ’yan wasan da suka ja ragamar ƙungiyar akwai Vincent Enyeama, Ahmed Musa, da John Obi Mikel.
6. Super Eagles ta buga kofin duniya a 2018
Najeriya ta buga gasar cin kofin duniya na 2018 amma kasar ta kare wasan cikin bakin ciki, bayan wata kwallon da Marcos Rojo na Argentina ya zura a mintuna na ƙarshe.
Zura kwallon ya tabbatar da cewa 'yan wasan Super Eagles sun kare a matsayi na uku a rukunin D a gasar da aka yi a kasar Rasha.

Source: Getty Images
Najeriya ta fafata da Croatia, Argentina da Iceland, inda ɗan wasan gaba Ahmed Musa ya haskaka sosai.

Kara karanta wannan
Wasanni nawa ya rage wa Najeriya ta shiga gasar cin kofin duniya? Bayanai sun fito
Ahmed Musa ya kafa tarihi a gasar, kasancewarsa ɗan Najeriya na farko da ya zura kwallo a gasanni biyu na Duniya—2014 da 2018.
2026: Congo ta hana Najeriya kai labari
A wani labarin, kun ji cewa kasar DR Congo ta doke Najeriya a wasan neman gurbin fafatawa a gasar kofin duniya ta 2026.
Hakan ya sanya Najeriya rasa gurbin fafatawa a gasar kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa karo biyu a jere.
Sai dai kocin Najeriya, Eric Chelle ya yi zargin cewa wani dan kasar DR Congo ya yi tsafi kafin samun nasarar doke Super Eagles.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


