Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa

Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa

Rayuwar auren Ahmed Musa ya kasance abun muhawaa ga mutane da dama. Imma ta fanni mai kyau ko akasin haka yana jan hankulan mutane da dama.

Ahmed Musa ya kasance kwararren dan kwallon kafa daga Najeriya wanda yake buga sahun gaba da gefe a tawagar kungiyar kwallon Saudiyya Al-Nassr sannan kuma yana cikin tawagar Super Eagles na Najeriya.

Musa ya zamo dan kwallon Najeriya na farko da ya zura kwallo a ragar wasa cin kofin duniya wato FIFA fiye da guda daya, bayan ya ci kwallo biyu a wasar da suka yi da Argenina a gasar FIFA na 2014.

Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa

Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa
Source: Depositphotos

Musa ya kuma kasance dan kwallon Najeriya na farko day a lashe gasar FIFA sau biyu, bayan ya zura kwallaye biyu a wasar da suka yi da Iceland a 2018.

Ahmed Musa ya yi aure sau biyu. Matarsa ta farko ta kasance Jamila Musa. Allah ya albarkace su da kyawawan yara biyu, mace da namiji. Sunan namiji Ahmed Musa Junior sannan mace kuma sunanta Halima Musa.

Sai dai, Ahmed da Jamila sun samu mumunan sabani wanda har ya kai ga musayar kalamai. Har ta kai yan sanda sun kama shi ina daga baya suka sako shi ya dawo gida.

Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa

Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa
Source: Depositphotos

Bayan haka sai Ahmed Musa ya sake aure inda ya auri amaryarsa Juliet Ejue.

Sun kuma cika shekara daya da aure a watan Mayu Ahmed ya bayyana cewa bai taba danasani a aurensa na farko a kuma cewa yana brin na biyun ya fin a farkon karko.

Allah ya kuma azurta Musa da Juliet da haihuwarsu na farko a tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel