El Clasico: Tarihi da Wasu Abubuwa kan Fafatawar Real Madrid da Barcelona
Jaridar Legit Hausa ta yi waiwaye kan lokuta 262 da aka fafata tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Barcelona a tarihi.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - El Clasico na daya daga cikin wasannin kwallon kafa mafi jan hankali a duniya, inda Real Madrid da Barcelona ke fafatawa a tarihi mai tsawo tun daga shekarar 1929.
Kulob din biyu sun fuskanci juna sau 262, inda Real Madrid ta fi Barcelona da nasara biyu kacal.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi waiwaye kan yadda kungiyoyin suka fafata a wasannin da suka buga tare.
Tarihin karawar Real Madrid da Barcelona
Shafin La liga ya wallafa cewa Real Madrid da Barcelona sun fafata sau 262 a tarihi, inda Madrid ta ci wasa 106, Barcelona kuma 104, kuma aka tashi kunnen doki sau 52.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lionel Messi ne ya fi cin kwallo a El Clasico yayin da Cristiano Ronaldo na kasar Portugal ke binsa a baya.

Source: Getty Images
A shekarar 2025, Barcelona ta doke Real Madrid sau uku a manyan gasa kafin Real ta dawo da martani da nasara 2-1 a Oktoban 2025.
Kafin kakar 2025, ita ma Real Madrid ta samu nasarori a kan Barcelona. Sai dai lamarin ya canza bayan an nada Hansi Flick.
Manyan fitattun ‘yan wasa a El Clasico
Rahoton da shafin MessivsRonaldo ya fitar ya ce Lionel Messi ne ke rike da kambun wanda ya fi cin kwallo a El Clasico, inda ya zura kwallo 26, Cristiano Ronaldo ya biyo shi a baya da kwallo 18.

Source: Getty Images
A shekaru bayan tafiyar Messi da Ronaldo, sabon salo ya shiga El Clasico inda sababbin ‘yan wasa kamar Vinícius Júnior, Jude Bellingham da Robert Lewandowski suka ke jan ragamar fafatawar.
Karawar Madrid da Barcelona a Laliga
A bangaren La Liga, Real Madrid ce ke gaba da nasarori 80, yayin da Barcelona ke da 76, kuma an tashi kunnen doki sau 35.
Real Madrid ta taba cin wasanni hudu a jere tsakanin Maris 2020 da Oktoba 2021, sannan ta ci uku daga cikin karawar su shida a gasar La Liga.

Source: Getty Images
Ba a taba tashi kunnen doki tsakanin kungiyoyin biyu ba tun Disamban 2019, abin da ke nuna cewa wasannin El Clasico suna yin zafi.
Wasanni 20 na karshe na Madrid da Barca
A shekarar 2020 zuwa 2021, Real Madrid ta ci Barcelona sau biyu da ci 3-1 da 2-1, sannan aka tashi 0-0 a Disamban 2019.
Shafin wasanni na StatMuse ya ce a 2022, kungiyar kwallon Barcelona ta doke Madrid da ci 4-0, kafin Madrid ta dauki fansa a Oktoba 2022 da ci 3-1.
A shekara ta 2023, kungiyoyin sun ci gaba da fafatawa, inda Barcelona ta ci 2-1 a Maris, Madrid ta mayar da martani da ci 4-0 a Copa del Rey, sannan ta sake ci 2-1 a Oktoba.

Source: Getty Images
A 2024, Madrid ta ci 3-2 a Afrilu, sannan ta ci 4-1 a Supercopa, amma Barcelona ta yi ramuwar gayya da ci 4-0 a Oktoba.
A 2025, Barcelona ta doke Madrid 5-2 a Supercopa, 3-2 a Copa del Rey, 4-3 a La Liga, sai dai Madrid ta dawo da karfinta da nasara 2-1 a Oktoba.
Wasan El-Clasico na karshe a Oktoban 2025
A shekarar 2025, Barcelona ta doke Real Madrid sau uku a manyan gasanni kafin Real Madrid ta samu nasara da 2-1 a Oktoban 2025.
Rahotanni sun nuna cewa Kylian Mbappe daJude Bellingham ne suka zurawa Barcelona kwallaye biyu a raga.
Messi na son buga kofin duniya a 2026
A wani rahoton, mun labarta muku cewa Lionel Messi ya nuna sha'awar sake taka leda a gasar kofin duniya da za a yi a 2026.
Legit Hausa ta gano cewa Lionel Messi ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a kasar Amurka.
Duk da ya nuna cewa yana son shiga gasar, Messi ya ce zai kara nazari tare da duba lafiyarsa kafin yanke matsayar karshe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



