WCQ: Kunkuru Ya Nuna Kasar da Za Ta Yi Nasara a Wasan Najeriya da Afrika Ta Kudu
- Najeriya da Afrika ta Kudu za su fafata a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2026, a yau Talata, 9 ga Satumba, 2025
- Tun a 2010 Bafana Bafana ke kokarin ganin ta shiga gasar kofin duniya, yayin da tawagar Super Eagles ta kasa shiga gasar baya
- Wani dattijon kunkuru mai shekaru akalla 196 ya yi hasashen kasar da za ta rashe wasan da za a fafata a filin wasa na Free State
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zanzibar – Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, za ta fafata da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026.
Tun bayan zuwan sabon koci, Eric Chelle, an ga canjin salo da tsari a tawagar Najeriya, abin da ya sa ake ganin kungiyar za ta iya shiga gasar a wannan karo.

Kara karanta wannan
Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko

Source: Getty Images
Nasarorin Najeriya a wasannin kofin duniya
Sai dai rashin fitaccen dan kwallon gaba, Victor Osimhen, a wasan Najeriya da Bafana Bafana, ya jefa jama’a cikin damuwa, ganin yadda yake taka muhimmiyar rawa a kowanne wasa, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Eric Chelle ya shahara tun bayan da ya dauki ragamar horar da 'yan wasan Super Eagles, inda kungiyar ta doke Rwanda 2-0 a Kigali, ta tashi 1-1 da Zimbabwe a Uyo.
Hakazalika Najeriya ta doke 'yan Amavubi da ci 1-0 ta hannun sabon dan wasan Wolves, Tolu Arokodare, wanda ya sa ake ganin cewa akwai ci gaba a karkashin jagorancin Eric.
Sai dai rashin Victor Osimhen, wanda ya fi kowanne dan wasa zura kwallo a raga, ya hana Najeriya samun sakamako mai kyau a wasu wasannin cancantar shiga gasar kofin duniya da suka gabata.
Kunkuru ya yi hasashen sakamakon wasan Najeriya
Wani tsohon kunkuru mai shekaru 196 da ke Prison Island a Zanzibar ya yi hasashen cewa Najeriya za ta zura kwallo biyu a ragar Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan
Najeriya, ƙasashe 9 za su fuskanci kusufin wata, an ji tsawon lokacin da zai dauka
Rahoton Sports247 ya ce wannan kunkuru shi ne mafi tsawon rai a duniya, kuma ya shahara wajen yin irin wannan hasashe.
Wannan ya kara daukar hankalin jama’a, musamman ma masoya Super Eagles da ke fatan ganin tawagar ta samu nasara.
Amma a kula, binciken Legit Hausa ya nuna cewa kunkuru mafi tsufan a duniya da aka sani shi ne Jonathan, mai shekaru 192, kuma yana zaune a tsibirin Saint Helena.

Source: Getty Images
Matsayi a teburin wasan shiga kofin duniya
A halin yanzu, Bafana Bafana suna kan gaba a teburin rukuni da maki 16, Benin Republic na matsayi na biyu da maki 11, yayin da Najeriya ke na uku da maki 10 kacal, inji rahoton TnTSports.
Wannan ke nuna cewa wasan da za a yi a yau 9 ga Satumba na da matukar muhimmanci ga Najeriya, domin samun nasara zai bude mata sabuwar dama ta shiga cikin gasar.
Mai tsaron ragar Najeriya, Stanley Nwabali, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Super Eagles na da karfin da za ta iya lallasa Bafana Bafana a gida da waje.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi daliban da aka sace lokacin Jonathan, ya ba su tallafin N1.85bn
NFF ta nada sabon kocin Super Eagles
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar ƙwallon ƙafan Najeriya ta Super Eagles ta samu sabon wanda zai riƙa horar da ƴan wasanta.
Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ta amince da naɗin Eric Sekou Chelle a matsayin sabon mai horar da ƴan wasan Super Eagles.
Naɗin Eric Sekou Chelle wanda tsohon kocin ƙasar Mali ne, zai fara aiki ne nan take daga ranar Talata, 7 ga watan Janairun shekarar 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng