Kunkuru mafi tsufa a nahiyar Afirka ya mutu ya na da shekara 344

Kunkuru mafi tsufa a nahiyar Afirka ya mutu ya na da shekara 344

Wani kunkuru mai shekaru 344 wanda aka fi sani da suna Alagba a fadar masarautar Soun dake Ogbomoso ta jihar Oyo ya mutu.

Kunkurun wanda aka yi ittifakin cewa shi ne kunkuru mafi tsufa a Afirka ya mutu ne ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 bayan yayi wata ‘yar gajeruwar jinya.

KU KARANTA:Rikicin Gabon da Amina Amal: Kotu ta sanya ranar da za ta yanke hukunci

Alagba ya yi suna kwarai da gaske kasancewarsa tun tsawon lokacin da kafa fadar ta Soun wadda a yanzu Oba Oladunni Oyewumi ke jagoranta.

Mun samu labarin cewa kunkurun yana da wurin kwanciya mai raid a laifya a lokacin rayuwarsa gabanin mutuwa ta zo masa.

Da yake tabbatar da labarin mutuwar Alagba, sakataren masarautar, Toyin Ajamu ya shaidawa manema labarai cewa, kunkurun wanda ke janyo ra’ayin jama’a da dama daga ciki da wajen Najeriya ze barwa masarautar kewarsa.

Ajamu ya ce: “Alagba ya rayu a wannan masarautar tsawon shekaru aru-aru. Ya kasance tamkar mai masaukin baki ga sarakuna da dama a wannan fada.”

A cewar sakataren, Alagba yana da tarihi mai yawan gaske wanda ya danganci fadar Soun gaba dayanta. Kari a kan wannan kuma ya ce, daga wurare daban-daban ake zuwa domin ziyartar kunkurun.

Haka zalika, sakataren ya bamu labarin cewa masarautar na shirin adana gawar Alagba domin ta kasance wani abin tarihi ga ‘yan baya.

https://www.dailytrust.com.ng/oyo-historic-344-year-old-tortoise-dies-at-souns-palace.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel