Kwallon Kafa: Lokuta 10 da Matan Najeriya Suka Lashe Kofin Zakarun Afrika
A makon da ya wuce kungiyar 'yan kwallon Najeriya mata (Super Falcons) ta lashe kofin zakarun Afrika karo na 10.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce Najeriya ta kara kafa tarihi bayan lashe gasar kofin zakarun Afrika na mata karon na 10.
'Yan kwallon Najeriya mata da aka sani da Super Falcons sun doke kasar Morocco da ci 3-2 a wasan karshe da aka fafata.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun tattaro muku bayanai da tarihin yadda 'yan Super Falcons suka samu nasara har sau 10 a wasan mata 'yan Afrika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. 1998: Farkon nasarar da ta kafa tarihi
The Nation ta rahoto cewa a shekarar 1998 ne Super Falcons suka fara kafa tarihinsu a gasar WAFCON bayan da suka lallasa Ghana da ci 2-0 a wasan karshe.
Wannan nasara ce ta farko da ta daukaka sunan Najeriya a kwallon kafa ta mata a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Source: Twitter
2. 2000: Najeriya ta kara samun nasara
A gasar 2000 da aka gudanar a Afrika ta Kudu, Super Falcons ta doke kasar a gida da ci 2-0 a wasan karshe.
Wannan ya sa Najeriya ta samu kofinta na biyu a jere, wanda ya karfafa matsayin ta na uwar gasar.

Source: Twitter
3. 2002: Najeriya ta ci kofin na 3 a jere
Najeriya ta ci gaba da nuna bajintarta a gasar 2002 da aka shirya a Najeriya, inda ta sake doke Ghana da ci 2-0 a wasan karshe.
Wannan ya zama kofinta na uku a jere kuma ya tabbatar da ragamar da suke da ita a gasar tun bayan farawa.

Source: Twitter
4. 2004: Falcons sun yi nasara karo na 4
A shekarar 2004, Najeriya ta sake zama zakara bayan da ta doke Cameroon da ci 5-0 a wasan karshe.
Wannan babbar nasara ta jaddada yadda Super Falcons ke mamaye gasar da kuma irin karfinsu a filin wasa.

Kara karanta wannan
An fara zanga zangar fatattakar ƴan Najeriya a Ghana, an faɗi laifuffukan da suke aikatawa

Source: Getty Images
5. 2006: Kofi na 5 ya daga darajar Najeriya
A gasar 2006 da aka yi a Najeriya, 'Yan Super Falcons sun doke Senegal a wasan kusa da na karshe sannan suka lallasa Ghana a wasan karshe da ci 1-0.
Duk da cewa a gidan Najeriya aka yi wasan, cin kofin ya nuna karfin da Super Falcons ke da shi a tsawon shekaru.

Source: Getty Images
6. 2010: Super Falcons sun dawo da karfinsu
Bayan an rashin cin nasarar su a 2008, Super Falcons sun dawo da karfinsu a 2010 da aka yi a Afrika ta Kudu.
Sun doke Equatorial Guinea da ci 4-2 a wasan karshe, inda suka kafa sabon tarihi na dawowa da karfi.

Source: Twitter
7. 2014: Najeriya ta lashe kofi na 7
Shafin Statisense ya wallafa a X cewa a gasar 2014 da aka yi a Namibia, Super Falcons sun doke Cameroon da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga.
Wannan karo sun nuna kwarewa, dabaru da hadin kai na gaske, wanda ya basu nasara ba tare da tangarda ba.

Source: Getty Images
8. 2016: Nasara ta 8 a Afrika
Najeriya ta sake lashe kofin a 2016 da aka gudanar a Cameroon, inda ta doke kasar a gida da ci 1-0 a wasan karshe.
Wannan ya zama kofinta na takwas, kuma ya ci gaba da tabbatar da kwarewar Super Falcons a fadin nahiyar Afrika

Source: Getty Images
9. 2018: Najeriya ta ci kofi na 9
A shekarar 2018, Super Falcons sun lashe kofin bayan sun doke Afrika ta Kudu a bugun finariti 4-3 bayan wasan ya tashi 0-0.
Wannan nasara ta tabbatar da cewa su ne zakarun gasar, kuma daga nan suka fara harin samun kofi karo na 10.

Source: Original
10. 2024 (An yi a 2025): Najeriya ta ci kofi na 10
A gasar 2024 da aka buga a 2025 a Morocco, Super Falcons sun doke masu masaukin baki da ci 3-2 a wasan karshe.
Wannan ya zama kofin su na 10 da Super Falcons suka yi burin samu bayan da suka nuna jarunta da kwazo.

Source: Twitter
Tinubu ya kalli wasan matan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya kalli wasan matan Najeriya da Morocco.
Tinubu ya bayyana cewa bai so kallon wasan ba saboda fargabar hawan jini amma wasu suka kunna talabijin a dakin shi.
Yayin da ya ke karbar 'yan wasan Super Falcons a fadar shugaban kasa, Bola Tinubu ya jinjina musu tare da ba su kyautar makudan kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


