Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Super Falcons, Ya Ba Kowa Kyautar N152.8m da Gidaje
- Shugaba Bola Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons da kyautar $100,000 da gidaje bayan sun lashe kofin WAFCON na 2025
- Shugaban kasar ya kuma ba 'yan wasan lambar girmamawa ta OON a liyafar da aka shirya masu a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Najeriya ta doke Morocco da ci 3-2 inda Esther, Folashade da Echegini suka zura kwallo uku bayan Morocco ta fara jan ragamar wasan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Bola Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons da lambar girmamawar kasa bayan sun lashe kofin mata na Afrika (WAFCON) 2025 da aka yi a kasar Morocco.
Shugaban ya ba kowacce ‘yar wasa kyautar dala $100,000 wacce ta yi daidai da N152,898,442 tare da gida mai dakuna uku, a matsayin karramawa kan kwazon da suka nuna.

Source: Getty Images
Tinubu ya karrama 'yan wasan Super Falcons
Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin sada zumunta, Olusegun Dada, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar 28 ga Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun Dada ya ce:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba kowacce ‘yar wasan 24 lambar girmamawa ta Officer of the Order of Niger (OON), tare da gidaje masu dakuna uku da kuma $100,000. Haka kuma, kowanne dan kwamitin kungiyar kwallon kafar ya samu kyautar $50,000.”
Shugaba Tinubu da uwargidansa Oluremi Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati sun tarbi 'yan wasan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban kasar ya yabawa jajircewar ‘yan wasan, inda ya kira su “jakadun fata-nagari” ga Najeriya.
Najeriya ta lashe kofin WAFCON a Morocco
A ranar 26 ga Yuli 2025, Super Falcons suka lashe kofin WAFCON karo na goma a tarihin su, bayan doke Morocco da ci 3-2 a filin wasanni na Rabat.
Morocco ce ta fara jan ragamar wasan da ci 2-0 cikin minti 24, kafin Najeriya ta dawo da karfinta tare da zura kwallaye uku a zagaye na biyu, inji rahoton Aljazeera.
Esther Okoronkwo ta fara farke ragar Morocco da cin kwallo mai kyau, sai Folashade Ijamilusi ta farke raga, kafin Jennifer Echegini ta tabbatar da nasarar Najeriya da kwallon karshe.
Shugaba Tinubu ya bayyana wannan nasara a matsayin misalin “jajurcewa ta dan Najeriya,” inda ya ce sun sanya farin ciki da kwarin gwiwa ga al’umma.

Source: Twitter
Yadda Tinubu ya biya 'yan wasan hakkokinsu
Bayan nasarar, an yi liyafa tare da nuna kofin a titunan Abuja, inda masoya suka rika daga tutoci suna rera wakoki na murna.
Kafin wasan karshe, Shugaba Tinubu ya tabbatar da biyan dukkanin alawus da hakkokin ‘yan wasan Super Falcons, kamar yadda shugaban hukumar wasanni ta kasa, Shehu Dikko, ya tabbatar.
Ana kyautata zaton cewa wannan mataki na Tinubu ne ya ba 'yan wasan damar maida hankali kacokan kan wasan ba tare da wata damuwa ba.
Tinubu ya gwangwaje 'yan wasan Super Eagles

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar Talata, 13 ga Fabrairu, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya karbi ‘yan wasan Super Eagles 25 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A wajen ganawar, shugaban ya karrama ‘yan wasan da lambar yabo ta Member of the Order of Niger (MON), tare da kyautar gida da fili ga kowane dan wasa.
Tawagar Super Eagles ta isa babban birnin tarayya Abuja, bayan da ta zo ta biyu a gasar bayan da ta sha kasa a hannun mai masaukin baki, Cote d'Ivoire.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

