Buhari ya taya Super Falcons murnar nasarar lashe kofin Afirka na bana
Shugaba Muhammadu Buhari ya taya kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya (Super Falcons) nasarar lashe kofin gasar kwallon kafa na mata na nahiyar Afrika (AWCON) na shekarar 2018.
Super Falcons din na Najeriya sunyi nasara ne a kan kungiyar Bayana Bayana na Afrika ta Kudu a daren yau bayan anyi tashi wasan ba ci ko daya amma akayi bugun da kai sai tsaron gida inda kungiyar Najeriya tayi nasara.
Wannan shine karo na uku da Super Falcons din ke lashe kofin a jere. Nasarar ta suka samu kuma ya basu damar zuwa gasar cin kofin duniya na mata wadda za ayi a kasar Faransa a shekarar 2019.
DUBA WANNAN: Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter @MBuhari, shugaban kasa ya ce: "Ina mika godiya ta ga masu horas da 'yan wasan, hukumar kwallon kafa na Najeriya (NFF), kungiyar masu goyon baya da kuma dukkan 'yan Najeriya masu kaunar kwallon kafa da suka bayar da gudunmawarsu ga jaruman Super Falcons din mu. Nayi imanin cewa 'yan Najeriya za suyi nasara duk lokacin da aka basu goyon cikaken goyon baya."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng