UCL: Malami Ya Yi Hasashen Arsenal a Wasan Karshe, Ya Fadi Mai Lashe Kofi

UCL: Malami Ya Yi Hasashen Arsenal a Wasan Karshe, Ya Fadi Mai Lashe Kofi

  • Malamin coci, Joel Atuma ya ce Arsenal za ta doke PSG a wasan kusa da karshe sannan ta fafata da Barcelona a gasar karshe ta UCL na 2025
  • A cewarsa, za a sake ganin karo tsakanin Arsenal da Barcelona kamar yadda ya faru a 2006, sai dai Arsenal za ta yi nasara yanzu
  • Hakan na zuwa da tsofaffin yan wasan Arsenal, Gael Clichy da Richard Matthew sun nuna kwarin gwiwa ga Arsenal

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - Wani malamin coci, Joel Atuma ya yi magana kan tasirin Arsenal a fadar zakarun Turai da za a gudanar a ranakun Talata da Laraba masu zuwa.

Faston ya bayyana hasashensa kan wasannin gasar zakarun Turai 2025 da ke tafe inda ya ce kungiyar Arsenal za ta doke PSG a filinta da ke birnin Paris a Faransa.

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

An yi hasashen wasan Arsenal a gasar zakarun Turai ta UCL
UCL: Malamin coci ya ce Arsenal za ta lashe kofin zakarun Turai. Hoto: Justin Setterfield / Getty Images via AFP.
Source: Getty Images

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a YouTube, Atuma ya bayyana cewa duniya za ta sake ganin wasan karshe kamar na shekarar 2006.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi hasashen wasan Arsenal a UCL

A 2006, kungiyar Barcelona ta doke Arsenal da ci 2-1 a wasan karshe na gasar, ta dauki kofinta karo na biyu kenan bayan daukar na farko a shekarar 1992.

Wannan nasarar ta kuma bude babi na lashe kofuna da dama ga Barcelona, inda suka dauki guda hudu cikin shekara goma.

Joel Atuma na 'The Lord Grace Provinces', ya ce Arsenal za ta doke PSG ta kai wasan karshe.

Malamin ya ce wannan wasan karshe zai kasance tsakanin Arsenal da Barcelona.

Ya ce:

"Zan fada muku, ku saurara, za ku ga karo tsakanin Arsenal da Barcelona kamar na da, Amma wannan karon Arsenal za ta ci.
An yi hasashen Arsenal za ta lashe gasar zakarun Turai
Malami ya ce Arsenal za ta lashe gasar zakarun Turai da ake yi yanzu. Hoto: Arsenal.
Source: Getty Images

Malami ya ce Arsenal za lashe UCL

Ina ji malamin zan tsaya nan, yana nufin Arsenal za ta dauki kofin wannan karon maimakon Barcelona kamar shekarar 2006.

Kara karanta wannan

Allah mai iko: Dattijuwa ƴar shekara 102 ta karbi Musulunci, an yaba da jajircewarta

Arsenal ta sha kashi 1-0 a hannun PSG a wasan farko na kusa da karshe a filin wasanta na Emirates da ke birnin London.

Martinelli da Trossard sun yi kokari wajen yunkurin cin kwallo amma ba su sami nasara ba a wasan farko.

Kungiyar da za ta iya haduwa da Arsenal

Idan Arsenal ta tsallake PSG, za ta kara da Inter Milan ko Barcelona a wasan karshe da za a yi a kasar Jamus.

Wasan zagaye na biyu tsakanin Barcelona da Inter Milan zai gudana a Italiya bayan sun tashi 3-3 a wasan farko a Sifaniya.

Tattaunawar Legit Hausa dan Arsenal

Adam Ahmad da aka fi sani da mai Gunners ya ce Fasto ya yi gaskiya a wannan babi.

Mai Gunners ya ce duba da yadda Arsenal ke taka kwallo a bana, akwai muhimmin abu da zai biyo baya.

Ya ce:

"Tabbas wasan PSG zai zo da kalubale amma a karshe Arsenal za ta yi nasara domin fafatawa a wasan karshe."

Ya bukaci magoya bayan Arsenal su kwantar da hankulansu bayan rashin nasara a gasar Firimiya.

Kara karanta wannan

Bayan sa'oi 30, an gaza kawo karshen gobarar da ta tashi a Isra'ila

Dan sanda ya mutu a kallon wasan Arsenal

A wani labarin, wani sufeto na ƴan sanda ya faɗi matacce ana tsaka da wasan Arsenal da Real Madrid a Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Abokinsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tare suke kallo kwallon kuma ɗan sanda ya yi murnar kowace kwallo da Arsenal ta jefa a ragar Madrid.

Ya ce sai da aka tashi wasan sannan suka fahimci ba ya motsi a kujerar da yake zaune, suka garzaya da shi asibiti amma aka tabbatar da ya mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.