Ya Naushi Alkalin Wasa: An Daure Tsohon Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Shekara 3
- Wata kotun Turkiyya ta yankewa Faruk Koca hukuncin zaman kurkuku na fiye da shekaru uku saboda naushin alkalin wasa
- Lamarin ya jawo fushin duniya, inda kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya ta dakatar da wasannin Super Lig na makonni
- Faruk Koca ya yi murabus daga matsayin shugaban Ankaragucu, amma kuma an ce zai daukaka karar hukuncin kotun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Turkiyya - Wata kotun Turkiyya ta daure tsohon shugaban kungiyar Super Lig shekaru sama da uku a gidan yari saboda ya naushin alkalin wasa.
Shugaban MKE Ankaragucu, Faruk Koca, ya naushi alkalin wasa, Halil Umut Meler a fuska bayan busa sautin tashi na wasan Super Lig a shekara ta 2023.
Menene abin da ya jawo naushin alkalin wasa?
Jaridar Goal.com ta rahoto cewa Faruk Koca, ya naushi Halil Meler bayan wasan da aka tashi da ci 1-1 tsakanin Caykur Rizespor da Ankaragucu a watan Disambar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda rahoto ya nuna, wata kotu a Ankara ta sami Koca da laifin "cin zarafin jami'in gwamnati" kuma ta yanke masa hukuncin shekaru uku da wata bakwai a kurkuku.
Me ya biyo bayan faruwar lamarin?
Lamarin ya jawo fushin duniya baki daya, inda kungiyar kwallon Kafa ta Turkiyya ta dakatar da dukkanin wasannin gasar na wasu makonni.
Koca ya yi murabus daga matsayin kocin kungiyar bayan lamarin, wanda ya bar alkalin wasan da rauni a gefen idonsa.
Kotun ta bayyana cewa an same shi da laifin dukan alkalin da kuma karya dokokin da aka kafa domin hana tashin hankali a wasanni.
Abin lura a wannan tirka tirka
An ci kungiyar Ankaragucu tarar Euro 45,000 sannan an tilasta musu su buga wasanni guda biyar ba tare da magoya bayansu a filin ba sakamakon wannan fitina.
Wannan ya faru ne bayan da Rizespor ta ci kwallo a mintin karshe na wasan. Daga bisani, Rizespor ta fita daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya a kakar wasan.
Me zai faru bayan yanke hukuncin?
Kotu ta kara da cewa, ta yankewa wasu mutane uku da ake tuhuma tare da Koca kan naushin alkalin wasan hukuncin zaman kurkuku na shekara daya zuwa biyar.
To sai dai kuma, rahotanni sun bayyana cewa Faruk Koca na shirin daukaka kara kan wannan hukunci, inda ya ce bai gamsu da matsayar kotun ba, inji rahoton ESPN.
'Yan kwallo da suka taba zaman yari
A wani lanarin, mun ruwaito cewa an samu wasu 'yan wasan kwallon kafa da aikata laifuffuka a ciki da wajen filin wasa kuma an yanke musu hukunci bisa doka.
Daga cikin 'yan wasa 10 da muka jero, akwai Ronaldinho, wanda aka kama shi da dan uwansa Roberto de Assis bisa laifin amfani da takardar fasfo na bogi a Paraguay.
Asali: Legit.ng