'Dan kwallo yayi sanadiyyar mutuwar Alkalin wasa saboda an sallame sa daga fili

'Dan kwallo yayi sanadiyyar mutuwar Alkalin wasa saboda an sallame sa daga fili

- Wani ‘Dan wasa yayi sanadin cikawar wani Alkalin kwallo

- Jan katin dai da aka ba wannan ‘Dan wasa ne ya fusata sa

- Hakan ya sa ya kar ma Alkalin kwallon har ta kai ya cika

Wani abin takaici ya faru kwanakin baya inda Alkalin wasa ya bakunci lahira a sanadiyyar jan katin da ya ba wani 'Dan wasa. Wannan abin bakin ciki ya faru ne a Kasar Mexico kamar yadda mu ka samu labari.

'Dan kwallo yayi sanadiyyar mutuwar Alkalin wasa saboda an sallame sa daga fili
Alkalin wasa yana ba wani 'dan kwallon Dortmund kati

Jose Valdemar Hernandez Capetillo ya garzaya barzahu a dalilin ba wani 'Dan kwallo kati. Alkali Hernandez Capetillo yayi mako guda a asibiti yana cikin gargara bayan harin da 'Dan wasan da ya sallama a cikin fili ya kai masa.

KU KARANTA: Wata ta nemi Alkali ya raba auren ta saboda soyayyar Mijin ta tayi yawa

Shugaban Alkalan wasa na Kasar Valentine Ramirez ya bayyanawa Jaridar The Sun News wannan inda yace Marigayin ya samu matsala a kwakwalwar sa bayan arangamar da su kayi da wani 'Dan wasa a filin kwallo na Pemex da ke Xalapa.

Ana dai wani karamin wasa ne da Kungiyar Guadalajara wannan mummunan abu ya faru. Yanzu ana kokarin ganin irin haka ya daina aukawa. Mun ji cewa an kama 'Dan wasan da yayi sanadiyyar rasuwar wannan Alkalin wasa daga baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng