Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa

- Magoya bayan kungiyar kwallon kafa a kasar Ghana sun lakadawa alkalan wasa duka har sun cire wa wani hakori

- Lamarin ya faru ne bayan an buga wasa tsakanin kungiyar Wanamafo Mighty Royals da Bofoakwa Tano a ranar 28 ga watan Maris

- Magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidansu ba su gamsu da yadda alkalin ya hura wasan ba hakan yasa suka far masa bayan an tashi

Fusatattun yan kallo sun lakadawa alkalan wasan kwallo duka a gasar wasar Division One a wasan da aka buga a mako na 14 a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, LIB ta ruwaito.

A cewar kafafen watsa labarai na kasar Ghana, lamarin ya faru ne bayan da kungiyar Wanamafo Mighty Royals suka buga wasa da Bofoakwa Tano aka tashi wasan ba tare da an saka kwallo a ragar kowa ba.

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa
Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shugabannin Kiristoci a Legas Sun Ce Suna Son Musulmi Ya Zama Gwamna a 2023

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa
Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa
Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Rahoton ya ce magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidanta sun afka cikin filin bayan an hura usur din tashi suka lakadawa jami'an wasan duka har ta kai ga rafari Niatire Suntuo Aziz ya rasa wasu daga cikin hakoransa.

A cewar Starr FM, maso kungiyar a gidanta ba su gamsu da yadda alkalin wasan ya yi aikinsa ba hakan yasa suka far masa da duka.

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

Kamar yadda hotunan ya nuna, alkalan sun fita hayyacinsu sakamakon harin da yan kallon suka kai musu bayan wasan.

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa
Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164