Shahararrun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 8 da Suka Fito daga Arewacin Najeriya
Yankin Arewacin Najeriya an san shi da samar da fitattun ƴan wasa waɗanda suka yi suna a harkar ƙwallon ƙafa.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƴan wasan da suke fitowa daga Arewa suna zama zakaru waɗanda ake labarinsu a cikin gida Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Jerin fitattun ƴan wasan Arewacin Najeriya
Jaridar Leadership ta tattaro jerin fitattun ƴan wasan ƙwallon ƙafa guda takwas da suka fito daga Arewacin Najeriya waɗanda suka zama sanannu a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Ahmed Musa
Ahmed Musa haifaffen birnin Jos ne na jihar Plateau. Ɗan wasan na gaba ya taka leda a kulobluka da dama a ciki da wajen Najeriya
Ahmed Musa shi ne ɗan wasan tawagar Super Eagles na farko da ya taɓa cin ƙwallo fiye da ɗaya a gasar cin kofin duniya.
Shi ne kuma ɗan wasan Super Eagles da ya taɓa cin ƙwallo a gasar kofin cin duniya har sau biyu, inda ya zura ƙwallo a gasar ta shekarar 2014 da kuma a gasar ta shekarar 2018, cewar rahoton SportsRation.
2. Umar Sadiq
Umar Sadiq haifaffen jihar Kaduna ne. Yana taka leda a kulob ɗin Real Sociedad na ƙasar Spain.
Ɗan wasan na gaba yana cikin tawagar ƴan wasan Najeriya ƴan ƙasa da shekara 23 da suka lashe tagulla a gasar Olympics ta shekarar 2016.
3. Alhassan Yusuf
Alhassan Yusuf haifaffen jihar Kano ne. Yana taka leda a kulob ɗin New England Revolution da ke ƙasar Amurka
Alhassan yana daga cikin ƴan wasan Super Eagles da suka zo na biyu a gasar AFCON 23 da aka buga a ƙasar Ivory Coast.
4. Zaidu Sanusi
Zaidu Sanusi haifaffen ƙaramar hukumar Jega ne a jihar Kebbi. Yana taka leda a kulob ɗin FC Porto na ƙasar Portugal.
Zaidu yana daga cikin ƴan wasan da ke taka leda a tawagar Super Eagles ta Najeriya.
5. Shehu Abdullahi
Shehu Abdullahi ɗan wasan baya ne wanda aka haifa a jihar Sokoto. Ya taka leda a kulobluka irin su, Kano Pillars da Levski Sofia.
6. Moses Simon
Moses Simon ɗan wasan gaba ne wanda aka haifa birnin Jos na jihar Plateau. Yana taka leda a kulob ɗin Nice na ƙasar France.
7. Jamilu Collins
Jamilu Collins haifaffen jihar Kaduna ne. Ɗan wasan na baya yana taka leda a kulob ɗin Cardiff City na ƙasar Wales.
8. Rabiu Ali
Rabiu Ali yana taka leda a kulob ɗin Kano Pillars a gasar Premier League ta Najeriya.
Rabiu Ali shi ne kyaftin ɗin ƙungiyar kuma ana yi masa kallon ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da kulob ɗin ke alfahari da su.
Ronaldo zai yi ritaya daga kwallo
A wani labarin kuma, kun ji cewa gabanin kocin Portugal, Roberto Martinez ya bayyana sunayen 'yan wasansa da za su fafata a gasar 'Nations League,' Cristiano Ronaldo ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga ƙwallo.
Tsohon dan wasan na Real Madrid da Manchester United ya ce har yanzu yana son ci gaba da bugawa ƙasarsa wasa amma idan lokacin ritayarsa ya zo, zai tabbata ya shirya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng