Super Eagles: Najeriya Za Ta Dauƙo Hayar Koci Daga Kasar Waje, Finidi George Ya Gaza

Super Eagles: Najeriya Za Ta Dauƙo Hayar Koci Daga Kasar Waje, Finidi George Ya Gaza

  • Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya ta yanke shawarar dauko hayar koci daga kasar waje domin horar da tawagar Super Eagles
  • Hukumar ta ce kocin ne zai taimakawa Super Eagles wajen ganin ta samu gurbin shiga gasar AFCON 2025 da gasar cin kofin duniya
  • Wannan na zuwa ne bayan da Super Eagles suka sha kashi a wasanni biyu jere yayin da suka gaza tabuka abin kirki a wasanni hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya (NFF) ta yanke shawarar dauko hayar mai horar da 'yan wasa daga Turai domin jan ragamar tawagar Super Eagles.

An ce NFF za ta dauko wa Super Eagles hayar koci daga Turai biyo bayan shan kashin da tawagar ta yi a wasanni biyu jere, karkashin Finidi George.

Kara karanta wannan

Abin farin ciki: Wata ƙasar Afrika ta fara haƙo mai a karon farko, an samu bayanai

Finidi George, kocin Super Eagles
Super Eagles: Najeriya za ta dauƙo hayar koci daga Turai. Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Super Eagles za ta samu sabon koci

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin zartarwar hukumar sun yanke wannan shawarar ne a wani taro da suka yi a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauko hayar sabon kocin zai taimakawa 'yan wasan Super Eagles a shirye-shiryen da take yi na wasannin sharar fagen cin kofin Nahiyar Afirka da na kofin duniya.

Wata sanarwar bayan taro da NFF ta fitar ta ce:

"Kwamitin ya yanke shawarar nemo masu horar da 'yan wasa da suka kware. Haka zalika za a samu sauye sauya a sashen kula da masu horar da 'yan wasan."

NFF ta ba da hakuri kan Super Eagles

Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko kocin Super Eagles na yanzu, Finidi George zai zauna karkashin kocin da za a kawo ko kuma za a kore shi gaba daya ba, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Hukumar NFF ta ba 'yan Najeriya hakuri kan rashin tabuka komai da tawagar Super Eagles ta yi a wasanni hudu cikin 10 na sharar fagen shiga gasar cin kofin duniya na 2026.

Haka zalika sanarwar ta jaddada himmatuwar NFF na yin duk mai yiwuwa domin ganin ta samu gurbin taka leda a gasar cin kofin Nahiyar Afirka da ma na gasar kofin duniya.

Za a sayawa Tinubu sabon jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta mika bukatar gaggawa na sayen sababbin jiragen sama guda biyu domin amfanin shugaban kasa da mataimakin sa.

Shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar, Ahmed Satomi, ya ce Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima na bukatar sabon jirgin sama saboda tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.