Forbes: Ronaldo Ya Zama Dan Wasa Mafi Samun Albashi a Duniya, Ana Biyansa $260M

Forbes: Ronaldo Ya Zama Dan Wasa Mafi Samun Albashi a Duniya, Ana Biyansa $260M

  • A cikin watanni 12, an ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya samu albashin dala miliyan 260
  • Wannan kuwa na zuwa ne yayin da kwantiragin Ronaldo da kungiyar Al Nassr ta samawa dan wasan dala miliyan 200 a kaka daya
  • An kuma gano Ronaldo ya samu karin dala miliyan 60 daga zama jakadan kamfanoni da suka hada da Nike, Binance da Herbalife

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daga shekaru takwas da suka gabata, lokacin da ya zama dan wasa mafi tsada a duniya a karon farko zuwa 2024, abubuwa da yawa sun canza a rayuwar Cristiano Ronaldo.

Ronaldo ya fara tashe ne a Real Madrid, daga bisani ya koma Juventus, sannan ya tafi Manchester United, in da yanzu yanzu ya ke taka leda a Al Nassr da ke Saudiya.

Kara karanta wannan

Emefiele: “Yadda na biya cin hancin $600, 000 domin a biya ni kudin kwangila a CBN”

Albashin Ronaldo a 2024
Albashin Ronalado a 2024 ya kai $260m, ya zama dan wasa mafi karbar albashi a duniya. Hoto: @Cristiano
Asali: Instagram

Amma duk inda ya tsinci kansa, abu ɗaya ne ke ci gaba da kasancewa a rayuwar Ronald; shi ne dan wasa mafi karbar albashi a duniya, in ji mujallar Forbes.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Ronalado ya samu albashin $260m

Ya samu kimanin dala miliyan 260 a cikin watanni 12 da suka wuce, wanda hakan ya sa a karo na hudu, ya sake zama dan wasa mafi yawan albashi a duniya.

Forbes ta kiyasta cewa, Ronaldo ya karbi dala miliyan 200 a wannan kakar a kwantiragin sa da kungiyar Al Nassr.

Kuma a matsayin daya daga cikin ’yan wasan da suka fi samun nasara a wasanni a duniya, Ronaldo ya samu karin dala miliyan 60 daga zama jakadan kamfanoni da suka hada da Nike, Binance da Herbalife.

Jerin 'yan wasa mafi karbar albashi

Domin tattara jerin 'yan wasan da suka fi samun albashi na wannan shekara, mujallar Forbes ta bi diddigin kudin da 'yan wasan suka samu tsakanin 1 ga Mayu, 2023, da Mayu 1, 2024.

Kara karanta wannan

A karon farko, an yi bikin nuna ado a Saudiyya da mata suka fitar da cinyoyinsu waje

Ga jerin 'yan wasa 10 mafi karbar albashi a duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa:

1. Cristiano Ronaldo - Kwallon kafa - Albashin $260m.

2. Jon Rahm - Wasan Golf - Albashin $218m.

3 Lionel Messi - Kwallon kafa - Albashin $135m.

4. LeBron James - Kwallon kwando - Albashin $128.2m.

5. Giannis Antetokounmpo - Kwallon kwando - Albashin $111m.

6. Kylian Mbappé - Kwallon kafa - Albashin $110m.

7. Neymar - Kwallon kafa - Albashin $108m.

8. Karim Benzema - Kwallon kafa - Albashin $106m.

9. Stephen Curry - Kwallon kwando - Albashin $102m.

10. Lamar Jackson - Kwallon karfi (NFL) - Albashin $100.5m.

Kwallon kafa: Mbappe zai bar PSG

A wani labarin, mun ruwaito dan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya tabbatar da cewa zai bar PSG a kakar wasa ta bana, inda zai koma Real Madrid.

An dauki watanni ba tare da sanin makomar Mbappe ba, amma yanzu an samu tabbaci a hukumance daga dan wasan da kansa cewa zai bar mahaifarsa zuwa Madrid.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel