Da N38m a kullum, Ronaldo ya zama ‘Dan wasan da ya fi kowa karbar albashi mai tsoka a Ingila

Da N38m a kullum, Ronaldo ya zama ‘Dan wasan da ya fi kowa karbar albashi mai tsoka a Ingila

  • Za a rika biyan Cristiano Ronaldo £480,000 a kowane mako a Old Trafford
  • Duk kasar Ingila babu ‘dan wasan da zai rika karbar albashi kamar Ronaldo
  • Ronaldo ya sha gaban Tauraron Man City, De Bruyne mai karbar £385,000

Cristiano Ronaldo zai zama ‘dan wasan kwallon kafan da ya fi kowa karbar albashi mai yawa a kasar Ingila, bayan komawarsa kungiyar Man United.

Metro UK ta ce har yau ‘dan wasan bai rattaba hannu a kan kwantiraginsa a kungiyar da ya bari a 2009 ba, duk da an ci ma yarjejeniya tun a makon jiya.

Nawa za a rika biyan Ronaldo?

Idan Ronaldo ya rattaba hannu a sabon kwatiragin, zai zama Manchester United ta shiga yarjejeniyar da ta fi kowane tsada a tarihin kulob din.

Jaridar Sun ta rahoto cewa ‘dan wasan gaban na Portugal zai rika karbar fam £480,000 duk mako, ma’ana sama da Naira miliyan 272 a kwana bakwai.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya yi wa Magoya-bayan Juventus maganar karshe, ya koma wasa a Old Trafford

Kamar yadda jaridar kasar wajen ta kawo rahoto a karshen makon da ya wuce, Ronaldo zai samu miliyan £24, 960,000 a shekara, sama da Naira biliyan 14.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da hakan yake nufi shi ne, Ronaldo zai rika samun kusan Naira miliyan 40 a kowace ranar Duniya.

Ronaldo
Ronaldo ya dawo gida Hoto: www.manchestereveningnews.co.uk
Asali: UGC

Da wannan kwantiragi, tsohon gwarzon na Man Utd da ya dawo gida, ya kere wa ‘dan wasan Manchester City, Kevin De Bruyne mai karbar £385,000 a mako.

‘Dan kwallon da ya fi kowa karbar albashi a Manchester United kafin nan shi ne David de Gea. Ana biyan ‘dan wasan mai tsaron raga miliyan £19.5 a shekara.

Rahotanni sun ce baya ga albashi, ‘dan wasan mai Ballon d’or biyar zai rika samun miliyoyin Daloli daga duk cinikin da Manchester Utd ta yi daga rigunansa.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya bukaci ya bar Juventus, ya na tangaririn neman wanda zai iya biyan albashinsa

Su wanene suka fi Ronaldo albashi?

Bayan barinsa Juventus, Tancredi Palmeri ya ce Cristiano Ronaldo ya sauko daga na biyu a sahun ‘yan kwallon da suka fi kowa albashi, ya sullubo zuwa na biyar.

1. Lionel Messi - Kungiyar PSG - €35m a shekara

2. Neymar Jr. - Kungiyar PSG - €30m a shekara

3. Andres Iniesta - Kungiyar Vissel Kobe - €25m a shekara

4. Oscar - Kungiyar Shanghai Port - €24m a shekara

5. Cristiano Ronaldo - Kungiyar Manchester United - €24m a shekara

Kun ji cewa a ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta, 2021, aka tabbatar da cewa Manchester United ta saye Cristiano Ronaldo daga kungiyar Juventus ta kasar Italiya.

A makon da ya wucen aka ji Cristiano Ronaldo ya aika wani sakon bankwana na musamman ga magoya bayan kungiyar Juventus, yayin da ya koma Manchester.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng