Real Madrid Ta Lashe Kofin La Liga Bayan Barcalona Ta Sha Kashi a Hannun Girona
- Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fitar da abokan hamayyarta na Sifaniya daga gasar La Liga bayan da ta lashe kofin a ranar Asabar
- Real Madrid ta lashe kofin na La Liga karo na 36 bayan doke Cadiz da ci 3-0 yayin da Barcelona ta sha kashi a hannun Girona da ci 4-2
- Carlo Ancelotti ya ce kungiyarsa ta Real Madrid ta cancanci lashe gasar La Liga duk da cewa tawagar ta samu kura-kurai a wasannin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Real Madrid ta lashe kofin La Liga karo na 36 bayan Barcelona ta sha kashi a hannun Girona da ci 4-2.
A ranar Asabar ne Madrid ta yi nasarar doke Cadiz da ci 3-0, wanda hakan ke nufin dole ne kungiyar ta Catalan ta yi nasara a Estadi Montilivi.
Bellingham ya taka rawa a nasarar Madrid
Barcelona ce ta jagoranci wasan da ci 2-1 a hutun rabin lokaci, amma kwallaye uku da Girona ta ci a zango na biyu ya taimakawa Real ta yi nasara, BBC ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham ya kasance jigo a nasarar da Madrid ta samu, inda ya zura kwallaye 18 a wasanni 26 a gasar La Liga a kakar wasansa na farko da kungiyar.
Bellingham ya wallafa a shafinsa na X, "CAMPEONES!!! HALA MADRID Y NADA MAS!!!" wanda ke nufin "Champions!!! Kun yi gaba Madrid kuma ba abin da ya rage!!!".
Carlo Ancelotti ya jinjinawa Madrid
AlJazeera ta ruwaito Carlo Ancelotti ya ce Real Madrid ta cancanci lashe gasar La Liga bayan ta doke Cadiz da ci 3-0 sannan Girona ta doke Barcelona da ci 4-2.
"Mun taka leda mai ban mamaki domin daga kofin La Liga. Mun yi 'yan kurakurai amma a karshe dai kwalliya ta biya kudin sabulu."
- Ancelotti ya fadawa manema labarai.
NFF ta nadawa Super Eagles sabon koci
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar kula da kwallon kafar Najeriya (NFF) ta nada Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagles.
An ruwaito cewa Finidi George, wanda tsohon dan wasan Eagles ne, ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga tsohon kocin tawagar, José Santos Peseiro.
Asali: Legit.ng