La-liga: Kungiyar Barcelona ta sauko daga tebur; Real Madrid ta yi sama

La-liga: Kungiyar Barcelona ta sauko daga tebur; Real Madrid ta yi sama

- Kungiyar Real Madrid ta doke Real Sociedad a gida da ci 1-2 a gasar La-liga

- Sergio Ramos da Karim Benzema sun taimakawa Zidane wajen samun nasara

- Ramos ya zura kwallonsa na 68 a La-liga – Hakan ya sa ya kafa sabon tarihi

Kungiyar Real Madrid ta yi amfani da damar da Barcelona ta yi watsi da shi a karshen makon nan wajen darewa saman teburin gasar La-liga, inda ta rufe ratar maki biyun da aka ba ta.

A ranar Juma’a ne Barcelona ta gaza doke kungiyar Sevilla bayan wasansu ya tashi 0-0. A wasan yau Lahadi, Real Madrid ba ta yi irin wannan sakaci ba a karawar da su ka yi da Sociedad.

Da wannan wasa da Real Madrid ta yi nasara ta ci 1-2, kungiyar Zinedine Zidane ta zama ta na kan maki guda da Barcelona watau 65, amma Real Madrid ce ta fi kowa yawan kwallaye.

Sergio Ramos ne wanda ya fara zurawa Real Madrid kwallo a raga a sakamakon finaritin da Vinicius ya samu. A minti na 70 Karim Benzema ya samu sa’a a kan ‘yan bayan Soceidad.

KU KARANTA: Ana rade-radin Ronaldo zai bar Juventus

La-liga: Kungiyar Barcelona ta sauko daga tebur; Real Madrid ta yi sama
Kungiyar Real Madrid
Asali: Getty Images

Ramos ya ci kwallonsa ta 68 a gasar Sifen ta La-liga, wannan ya sa ya zarce ‘yan wasan baya irinsu Ronald Koeman, Fernando Heiro da Roberto Carlos a wajen yawan kwallaye a raga.

Real Socieded sun nemi su tada hankalin Real Madrid da su ka zo bakunci yayin da ake saura mintuna bakwai a tashi wasa. Merino ne ya jefawa Thibaut Courtois kwallo a minti na 83.

A karshe dai haka aka tashi wannan wasa da aka gwabza a filin wasan Reale Arena. A tarihin Sifen, ba a taba samun 'dan wasan bayan da ya ke da adadin kwallayen Sergio Ramos ba.

Yanzu wasanni takwas ne su ka rage a gasar La-liga, inda abubuwa su ka cigaba da tafiya a haka, Real Madrid za ta zama zakarar wannan shekara a karkashin mai horaswa Zinedine Zidane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel