Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasar Andolus, wacce aka fi sani da 'Spain', a karo na 34 bayan ta lallasa kungiyar Villareal a dare ranar Alhamis da ci 2 -1.
Dan wasa gaba na kungiyar Real Madrid, Karim Benzema, ya saka kwallo biyu a wasansu da Villareal, wanda ya basu nasarar bawa kungiyar Barcelona tazarar maki bakwai a teburin jerin kungiyoyin kwallon kafa na gasar Laliga.
Real Madrida ta samu nasarar kwace kofin Laliga daga hannun babbar abokiyar hamayyarta, kungiyar Barcelona wacce ke rike da kofin a kakannin wasa biyu da suka gabata.

Real Madrid ta lashe kofin gasar Laliga a karo na 34
Source: Getty Images
A wani labarin wasan kwallon kafa da Legit.ng ta wallafa, kungiyar Tottenham da ke kasar Ingila ta samu nasara a kan Kungiyar Newcastle da ci 3-1.
Nasarar ta Tottenham, ita ce ta farko da Jose Mourinho ya dandana a gida a gasar Firimiya tun da ya fara horaswa a kasar Ingila.
DUBA WANNAN: 'Yanta mayakan Boko Haram 602: Sai da mu ka rantsar dasu kafin sakinsu - DHQ
Jose Mourinho ya doke Newcastle a gidanta na St James Park wannan karo bayan ya jarraba sa’arsa sau takwas bai dace ba a baya.
Kafin yanzu, Jose Mourinho ya gwabza da Newcastle da kungiyoyin Chelsea da Manchester United, amma duk bai taba samun maki uku a kan kungiyar ba.
“Su na wasa da kyau, sun san yadda ake kwallo, sun san yadda za su samu maki, su na da hadari ta wurare daban-daban.” Mourinho game da Tottenham.
Da aka yi wa kocin magana game da wannan nasara mai tarihi da ya samu, ya bayyana cewa ba a jiya ne ya fara doke Newcasle a gida ba, ya yi hakan a lokacin da ya ke Chelsea.
Jose Mourinho ya tabbatar da cewa ya taba cin wasanni biyu a filin St James Park a wasan karamin kofi.
An yi haka a watan Nuwamban shekarar 2004, an kuma maimaita a Disamban shekarar 2006.
Sai dai, a ranar Laraba, 15 ga watan Yuli ne Mourinho ya fara samun sa’a a kan Newcastle a gidanta a gasar Firimiya.
Tsohon kocin na Real Madrid da Inter Milan ya yi amfani da wannan dama ta jiya, ya yabawa tsohon mai gidansa, Bobby Robson wanda ya daura shi a kan hanya.
Kocin ya yi aiki da Bobby Robson a matsayin tafinta a Porto da Sporting Lisbon kafin ya zama mataimakin mai horaswa, daga nan ne tauraruwarsa ta rika haskawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng