Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Ta Nada Sabon Kocin Tawagar Super Eagles

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Ta Nada Sabon Kocin Tawagar Super Eagles

  • Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada tsohon dan wasan Super Eagles Finidi George a matsayin sabon kocin kungiyar
  • An ruwaito cewa Finidi George, ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga tsohon kocin Super Eagles, José Santos Peseiro
  • Babban aikin sabon kocin shi ne jagorantar tawagar Najeriya zuwa ga nasarar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotannin da muka samu yanzu na nuni da cewa an nada Finidi George a matsayin sabon kocin tawagar Najeriya ta Super Eagles.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sanar da nadin Finidi a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da mace mafi tsayi a duniya ta rigamu gidan gaskiya a kasar Brazil

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada sabon kocin tawagar Super Eagles
Hukumar NFF ta nada Finidi George a matsayin sabon mai horar da tawagar Super Eagles. Hoto: @thenff
Asali: Twitter

Finidi ya rike kocin rikon kwarya

Finidi George, wanda ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga José Santos Peseiro ya kasance kocin rikon kwarya bayan tafiyar dan kasar Portugal din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta rahoto cewa cikin wa'adinsa na wucin gadi, George ya jagoranci wasanni biyu na sada zumunta a Morocco a watan da ya gabata.

Tawagar ta kawo karshen rashin nasara na tsawon shekaru 18 tsakaninta da Ghana inda wasan ya tashi da ci 2-1, amma George ya sha kashi a hannun Mali da ci 0-2.

Nasarorin da Finidi ya samu a taka leda

Fitaccen dan wasan ƙwallon ƙafa, George, ya samu tarin lambobin yabo da suka hada da lambobin zinare, azurfa da tagulla daga gasar AFCON 1992, 1994, 2000 da 2002.

Daya daga cikin abubuwan tunawa da George shi ne taimakawa marigayi Rashidi Yekini wajen zira kwallon farko ta Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA a karawarta da Bulgaria a Dallas, Amurka a ranar 19 ga Yuni 1994.

Kara karanta wannan

Naira tayi zuciya, darajar kudin Najeriya ta farfado a kasuwar canji

Aikin da ke gaban sabon kocin S/Eagles

Babban aikin sabon kocin shi ne jagorantar kungiyar zuwa ga nasara a wasanni biyu masu muhimmanci na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA 2026.

Najeriya za ta kara tsakaninta da Afrika ta Kudu da Jamhuriyar Benin a Uyo da Abidjan, cikin makonni biyar masu zuwa, rahoton jaridar Leadership.

An nada kocin Golden Eaglets

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa Manu Garba ya zama sabon mai horar da tawagar 'yan kasa da shekaru 17 ta Najeriya (Golden Eaglets).

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sanar da nadin Garba wanda ya taba jagorantar tawagar zuwa ga nasarar lashe gasar kofin duniya na 2013.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.