AFCON 2023: Ahmed Musa Ya Aike da Sako Mai Ratsa Zuciya Bayan Rashin Nasarar Najeriya a Wasan Karshe
- Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya yi tsokaci kan rawar da tawagar Najeriya ta taka a gasar AFCON 2023
- Musa ya ce duk da rashin nasara a hannun Ivory Coast mai masaukin baƙi, yana cike da alfahari saboda Super Eagles na Najeriya
- Tsohon ɗan wasan gaban na CSKA Moscow da Leicester City ya yaba da haɗin kan ƙungiyar a filin wasa wanda ya ce ya wuce bambance-bambancen addini da ƙabilanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Abidjan, Cote d’Ivoire - Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, ya yaba da ƙoƙarin da ƴan wasan Super Eagles suka yi a gasar AFCON 2023.
Musa, wanda bai taka leda ko sau ɗaya ba, ya ce takwarorinsa sun nuna "juriya da jajircewa a yayin gasar".
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa da ya yi suna a Kano Pillars ya yabawa ƴan Najeriya bisa sadaukarwa da goyon bayan da suka bayar a gasar AFCON 2023 da aka kammala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Ahmed Musa ya ce kan rashin nasarar Najeriya?
Musa mai shekara 31 a duniya ya bayyana hakan ne dai a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani a baya da Twitter).
Wani ɓangare na rubutun na cewa:
"Idan muka yi la’akari da tafiyar da muka yi a gasar AFCON, ina cike da alfahari sbaoda ƴan wasan Super Eagles na Najeriya, duk da cewa ta yiwu mun gaza zama zakaru, haɗin kan mu a filin wasa ya wuce bambance-bambancen addini da na ƙabilanci, wanda ya tunatar da mu ƙarfin ƙwallon ƙafa na haɗa kawunanmu.
"Ga dukkan magoya bayanmu masu ban sha'awa, sadaukarwarku da rera waƙoƙinku sun ƙara mana ƙarfin gwiwa fiye da kowane lokaci, sha'awarku game da wasan da kuma ƙasarmu haƙiƙa yana da ban sha'awa.
Atiku da Obi sun aike da sako mai muhimmanci kan rashin nasarar Super Eagles a wasan karshe na AFCON
"A lokacin da mu ke cikin halin matsin tattalin arziƙi, mu ci gaba da nuna irin wannan ɗabi'ar haɗin kan ba a filin wasa kawai ba, har a sauran kowane ɓangare na rayuwarmu."
Karanta ƙarin abubuwa kan AFCON 2023
- Atiku da Obi sun aike da sako mai muhimmanci kan rashin nasarar Super Eagles a wasan karshe na AFCON
- AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe
- Muhimmin dalilin 1 da ya sa Ivory Coast ta doke Najeriya a wasan ƙarshe na kofin AFCON
Najeriya Ta Yi Rashin Nasara a Hannun Ivory Coast
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar Super Eagles ta Najeroya ta yi rashin nasara a hannun The Elephants na Ivory Coast a wasan ƙarshe na gasar AFCON 2023.
Ivory Coast mai masaukin baƙi dai ta doke Najeriya da ci 2-1, wasan ƙarshen da aka gudanar da filin wasa na Alassane Outtara dake birnin Abidjan.
Asali: Legit.ng