'Dan wasan Chelsea Ngolo Kante yayi hadari a hanyar zuwa filin wasa

'Dan wasan Chelsea Ngolo Kante yayi hadari a hanyar zuwa filin wasa

- ‘Dan wasan tsakiyan Chelsea yayi hadarin mota a Garin Landan

- Ngolo Kante yayi hadari ne yayin da ake shirin buga wani wasa

- ‘Dan kwallon na Faransa bai samu wani rauni daga hadarin ba

Wani babban Dan wasan Kungiyar kwallon kafa na Chelsea yayi hadari a hanyar zuwa wasa a filin Stamford Bridge da ke cikin Landan inda za su kara da Kungiyar Arsenal a wani wasan Kofi.

'Dan wasan Chelsea Ngolo Kante yayi hadari a hanyar zuwa filin wasa
‘Dan wasa Kante ya gamu da hadarin mota

Ngolo Kante yayi hadarin mota a kan hanyar karawar su da Arsenal inda aka tashi wasan 0-0. ‘Dan wasan mai shekaru 26 yayi karo ne da wata katuwar mota gingimari a kan hanyar titin Kings Road da ke Yammacin Birnin Landan.

KU KARANTA: 'Yan kwallon Kwara United sun yi hadari a hanyar Legas

An dai dace ‘Dan wasan tsakiyar da Chelsea ta saya daga Leicester kan kudi kusan Dala Miliyan $40 a bara bai samu wani rauni daga hadarin ba. Wani ‘dan ta’aliki ya dauko hoto lokacin da wannan abu ya faru a cikin Gari.

Abin da ya burge Jama’a shi ne duk 'Dan wasan na Chelsea yana samun albashi mai tsoka na sama da Dala $100,000 a kowane mako amma karamar motar nan ta Mini Cooper S yake hawa wanda ba ta wuce Dala $20,000 ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng