AFCON: Ahmed Musa Ya Yi Magana Kan Makomarsa Bayan Kammala Gasar, Ya Bai Wa Jama’a Mamaki

AFCON: Ahmed Musa Ya Yi Magana Kan Makomarsa Bayan Kammala Gasar, Ya Bai Wa Jama’a Mamaki

  • Dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya yi magana kan matakin da zai dauka bayan kammala gasar AFCON a yau Lahadi
  • Musa wanda shi ne kyaftin din tawagar Super Eagles ya ce ba shi da niyyar barin tawagar a yanzu tun da ya na buga kwallo
  • Dan wasan wanda ke neman cin kofin AFCON a karo na biyu bai taba buga ko da wasa daya ba a wannan gasa da ake yi a Ivory Coast

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ivory Coast – Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya ce ba ya tsammanin barin kungiyar nan kusa.

Musa wanda ke neman cin kofin AFCON a karo na biyu bai taba buga ko da wasa daya ba a wannan gasa da ake yi a Ivory Coast.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Malamin da ya yi hasashen nasarar Tinubu, ya yi magana kan Osimhen

Ahmed Musa ya yi magana kan makomarsa bayan kammala gasar AFCON
Ahmed Musa ya ce ba shi da niyyar barin Super Eages a yanzu. Hoto: Ahmed Musa.
Asali: Getty Images

Mene Ahmed Musa ke cewa?

Dan wasan mai shekaru 31 da ke buga wasa a kungiyar Sivasspor da ke Turkiya ya ce har yanzu dan wasa ne shi kuma idan aka sake kiransa zai amsa gayyata a gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Ba na shirin barin tawagar a yanzu saboda har yanzu ni dan wasa ne, ina buga wasa, idan kocin ya gayyace ni zan amsa gayyatar a gaba.”

Ahmed ya ce ba ya damuwa saboda rashin buga wasa a gasar inda ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne nasarar tawagar Super Eagles a gare shi, cewar The Nation.

Ya fadi abin da ya fi muhimmanci a yanzu

Ya kara da cewa:

“Mutane da suka sanni sun san ni mutum ne mai hakuri, na buga wasa a kungiya da kuma kasa don yin nasara nima yanzu wasu za su buga don samo mana nasara.

Kara karanta wannan

AFCON" 'Dan Najeriya ya yi hasashen sakamakon wasan karshe tsakanin Najeriya da Ivory Coast

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne nasara, komai zai iya faruwa a gaba, ni dan wasa ne wanda ya ke biyayya ga duk abin da koci ya ce, ba ni da matsala.”

Wannan na zuwa ne yayin da tawagar za ta buga wasan karshe a yau Lahadi 11 ga watan Faburairu da kasar Ivory Coast mai masaukin baki, cewar Daily Trust.

Musa ya jagoranci addu’a

Kun ji cewa, Kyaftin din tawagar Super Eagles ya jagoranci addu’a ga ‘yan Najeriya biyar da suka mutu yayin wasan Najeriya.

Musa ya yi addu’ar rahama ga wadanda suka mutu inda ya yi alkawarin da yardar Allah za su dawo da kofin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.