AFCON: ‘Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Sakamakon Wasan Karshe Tsakanin Najeriya da Ivory Coast
- Hankula sun karkata kan wani 'dan Najeriya, wanda ya yi hasashen cewa Najeriya za ta doke Senegal a a cikin mintuna 90 a soshiyal midiya
- Ya yada wani bidiyo inda ya tantance makomar Super Eagles tare da bayar da tabbacin cewa Najeriya za ta kaucewa karin lokaci
- Najeriya za ta so sake yin nasara karo na hudu a gadar AFCON a ranar Lahadi yayin da za ta kara da mai masaukin baki Ivory Coast
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani 'dan Najeriya ya yi fice a dandalin soshiyal midiya bayan ya yi hasashen yadda karon Najeriya da Ivory Coast za ta kaya a wasan matakin rukuni.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa kafin wasan, mutumin ya yi nazarin karfin kungiyar tare da bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara a cikin lokaci.
A wani bidiyo da @thehindsightpod ya wallafa, ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya ba za ta bukaci karin lokaci ko fenariti ba don yin nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu Najeriya za ta kara da mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe a ranar Lahadi, tana mai fatan nasara a karo na hudu a gasar AFCON.
Tuni dai Najeriya ta doke Ivory Coast da ci 1-0 a matakin rukuni, wanda hakan ya bata dama kan abokan karawarta.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Ufiumarfaruk ya ce:
"Wannan mutumin dattijo ne jinjina yallabai."
Dynamic Range:
"Babban mutum!!"
Okeemegor:
"Cikakken lokaci Najeriya 2- 2 Ivory coast. Osimhen zai ci kwallo na uku amma za a soke 1. Wannan shine abin da na gani, zan dawo kan wannan bayan wasan. Oshimhen zai zura kwallo Najeriya za ta yi nasara kan fenariti."
SportPremi:
“Ivory Coast 0-2 Najeriya.”
Malami ya fadi kasar da za ta ci gasar AFCON
A wani labarin, mun ji cewa shahararren Fasto, Dakta Kan Ebube Muonso ya yi hasashen kasar da za ta lashe gasar AFCON a gobe Lahadi 11 ga watan Faburairu.
Ebube ya ce kasar Ivory Coast za ta tafi da kofin gida sai dai hakan zai faru ne a cikin kuskure.
Asali: Legit.ng