AFCON: Tauraron S/Eagles, Osimhen Ya Samu Matsala Za a Buga Wasan Afrika ta Kudu

AFCON: Tauraron S/Eagles, Osimhen Ya Samu Matsala Za a Buga Wasan Afrika ta Kudu

  • Victor Osimhen bai iya bin jirgin da ya dauki ‘yan wasan Super Eagles daga Abidjan zuwa Bouke ba
  • ‘Dan wasan kwallon kafan na kungiyar Napoli yana fama da ciwon ciki, an bar shi a hannun likitoci
  • Da zarar ‘dan kwallon ya warke, zai bi abokan aikinsa domin ya shirya tunkarar kasar Afrika ta Kudu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - ‘Dan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen bai cikin tawagar Najeriya da ta wuce birnin Bouaké a kasar Ivory Coast.

Rahoton Goal.com ya nuna ‘yan wasan Super Eagles sun tafi Bouaké inda za su gwabza da tawagar Bafana Bafana a gasar AFCON.

Osimhen
Victor Osimhen a AFCON 23: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

AFCON: Victor Osimhen babu lafiya

Sai dai Victor Osimhen bai samu tafiya ba, an bar shi a Abidjan inda aka yi wasan Najeriya da kasar Angola da Super Eagles ta ci 1-0.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya shaidawa Tinubu abin da ake bukata da gaggawa domin zaman lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan wasan na Napoli ya buga duka wasanni biyar da Super Eagles ta buga a gasar cin kofin nahiyar na Afrika watau AFCON 2023.

Osimhen zai dawo cikin Sper Eagles?

Tauraron ya ci kwallo daya ne kurum kuma ya bada an ci guda, amma yana cikin manyan ‘yan wasan da Najeriya ta ke takama da su.

Jawabin da ya fito daga Super Eagles ya ce ban da ‘dan wasan mai shekara 25 jirginsu ya tafi Bouake domin shirin wasan Laraba.

Sanarwar da Super Eagles ta fitar

Jaridar The Athletic ta ce ‘dan kwallon yana fama da ciwon ciki, saboda haka aka bar shi a hannun likitocin Super Eagles a Abidjan.

Idan an samu ya warke sarai da safe, sanarwar ta ce Osimhen zai kama hanya ya bi takwarorinsa kafin karfe 5:00 na yammacin yau.

Kara karanta wannan

Buhari ne sanadi: Jagora a APC ya fadi wanda ya jefa tattalin Najeriya a mawuyacin hali

Najeriya ta na da tulin ‘yan wasan gaba wadanda ba su buga ko wasa guda a AFCON ba. Super Eagles na cikin masu harin gasar bana.

Daga cikinsu akwai Ahmed Musa mai rike da kambun Eagles. Wasu suna ganin ya kamata Koci Jose Peseiro ya rika amfani da shi.

Ahmed Musa da Super Eagles

Ahmed Musa mai shekara 31 bai buga wasa a Ivory Coast ba, amma an ji yadda yake taimakawa 'yan kwallon Najeriya a gasar bana.

A ranar Larabar nan Najeriya za ta gwabza da Afrika ta Kudu a wasan daf da karshe. Ivory Coast kuma za ta kara da kasar DR Congo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng