AFCON 2023: Bature Ya Fadi Makomar Tawagar Najeriya a Wasan da Za Ta Buga da Afrika Ta Kudu
- Wani bature ya yi hasashen sakamakon wasannin kusa da na karshe da za a buga a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi
- A wasan farko da ya hada Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, ya fadi sakamon wasan da dan wasan da zai zura kwallo a raga
- Hasashen da ya yi na wasannin biyu bai yi wa wasu masoya kwallon kafa dadi ba, yayin da wasu kuma suka ba da nasu hasashen
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gabanin wasannin kusa da na karshe, wani bature ya yi hasashen kungiyoyin da za su kai ga wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu.
A cikin wani faifan bidiyo na TikTok, @callum_wm ya ce wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu zai kare ne da ci daya mai ban haushi.
Najeriya da Ivory Coast za su je wasan karshe
@callum_wm ya bayyana cewa Najeriya ce za ta yi nasara inda dan wasan Fulham Alexander Chuka Iwobi ne zai zura kwallo daya tilo a wasan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasa na biyu da ya kunshi Ivory Coast da DR Congo kuwa, @callum_wm ya ce za a kawo karshen wasan da ci biyu da nema.
Ya ce Nicolas Pepe ne zai zura kwallayen da tawagar Ivory Coast za ci.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun mayar da martani kan hasashen baturen:
Raja ya ce:
"Za ka sha mamaki."
Simply pc ya ce:
"Ubangiji ka amsa hasashen mutumin nan, tabbas muna fatan Najeriya ce za ta ci wasan."
User256 ya ce:
"Dr Congo za ta lashe kofin, ku dai tsaya nan kuna kallo."
Riri ya ce:
"Ba yadda za a yi mu yi nasara a kan SA da wannan mai tsaron gidan nasu a raga."
Mai tsaron ragar Afrika ta Kudu ya shirya karawa da Super Eagles
A wani labarin, mai tsaron ragar tawagar Afrika ta Kudu, Ronwen Williams ya ce ya shirya karawa da Super Eagles ta Najeriya a wasan kusa da na karshe.
A ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu ne za a buga wasannin kusa da na karshe a gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2023.
Asali: Legit.ng