Jerin Kasashe 8 Da Ba Su Taba Lashe Kofin AFCON Ba

Jerin Kasashe 8 Da Ba Su Taba Lashe Kofin AFCON Ba

  • A yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin Nahiyar Afirka na 2023, akwai kasashen Afrika da ba su taba cin kofin AFCON ba
  • Kasar Namibiya na daga cikin kasashen ta kafa tarihi a gasar a ranar Talata, inda suka samu nasarar su ta farko tun da aka fara gasar
  • Legit Hausa ta tattaro jerin kasashe 8 da ba su taba cin kofin AFCON ba, wasu ma kasashen basu taba buga wasa a gasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) 2023 ta fara da abubuwan ban mamaki yayin da wasu manyan kasashe kamar Ghana da Aljeriya suka fice daga gasar.

Yayin da za a fara buga zagaye na 16 na gasar a ranar Asabar mai zuwa, Legit Hausa ta yi dubi kan wasu kasashe da ba su taba lashe gasar ba, kamar yadda Sports Brief ta ruwaito.

Kara karanta wannan

AFCON: Jerin tawagar kasashe 10 da suka tsallake zuwa zagaye na 16

Jerin kasashe takwas da basu taba lashe gasar AFCON ba
Jerin kasashe takwas da basu taba lashe gasar AFCON ba
Asali: Getty Images

Namibiya ta kafa tarihi a gasar cin kofin Afrika a ranar Talata 16 ga watan Janairu, lokacin da ta samu nasarar a gasar a karon farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasar da ke a yankin Afirka ta Kudu tana cikin rukunin E na gasar ta 2023.

Jerin kasashe takwas da basu taba lashe gasar AFCON ba

1. Eritrea

Eritiriya na daga cikin jerin kasashen da ba su taba samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ba.

Karancin kayayyakin wasan kwallon kafa na kasar sun yi tasiri kan rashin halartar su gasar.

2. Sudan ta Kudu

Kamar Eritriya, ita ma Sudan ta Kudu, mai mafi karancin shekaru a kasashen Afirka ba ta taba shiga gasar AFCON ba.

3. Madagascar

Kasar wadda ke kan tsibiri ta fara buga gasar AFCON a shekarar 2019. Yayin da suka taka rawar gani a lokacin, ba su iya samun nasara ba.

Kara karanta wannan

Ya ci kudin banki: Kotu ta daure wani dan jihar Bauchi shekara 3 a gidan yari, an samu bayani

A lokacin, sun yi canjaras sau daya kuma sun yi rashin nasara sau biyu wanda ya sa su ficewa a gasar.

4. Comoros

Comoros na cikin rukunin C na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2021, da aka yi a watan Janairu da Fabrairun 2022 a Kamaru.

Sun sha kashi a wasansu na farko a hannun Gabon da ci 1-0. Wasa na biyu kuma ya kare da ci 2-0, inda suka sha kashi a hannun Morocco.

5. Seychelles

Ita kuwa tawagar Seychelles, sun je har zagayen wasannin share fage, sai dai ba su taba kaiwa wasan karshe ba.

6. Laberiya

Kasar da ta ke a yankin Afirka ta Yamma ta samu tikitin shiga gasar sau hudu. Sai dai ba ta taba tsallakawa zuwa matakin wasannin zagaye na 16 ba.

7. Gambiya

Scorpions sun shiga gasar AFCON ta 2021 amma sun kasa samun nasarar wasan su na farko.

Har yanzu ba su iya samun nasara a gasar kofin na 2023 da ke kan gudana, inda ta yi rashin nasara a dukkan wasannin ta uku, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

AFCON: Kwankwaso ya taya tawagar Najeriya nasarar hayewa mataki na gaba

8. Mauritaniya

Mauritania na ci gaba da neman nasarar farko a gasar AFCON a hukumance a yayin da ta ke neman tsallakawa zuwa zagayen na 16 na gasar.

A baya dai kungiyar ta yi canjaras sau uku a gasar amma har yanzu bata samu nasara ba, inda ta sha kashi da ci 1-0 a wasansu na farko da Burkina Faso.

AFCON: Jerin kasashe 10 da suka tsallake zuwa zagaye na 16

A wani labarin makamancin wannan, akalla kasashe 10 ne zuwa yanzu suka samu nasarar cin wasannin su a matakin rukunai na A zuwa E, yayin da suka tsallaka zuwa zagaye na 16.

Najeriya, Senegal na daga cikin kasashen da suka yi nasara, kamar yadda Legit Hausa ta tattara bayanan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.