Najeriya ta kafa tarihi a gasar cin kofin nahiyar Afrika na 2019
Najeriya ta zama kasa ta farko da ta kai ga zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen nahiyar Afrika (AFCON) na shekarar nan, 2019.
Ana buga gasar ta wannan shekarar a kasar Masar (Egypt).
Najeriya ce kasar da ta fara kai wa ga zagaye na biyu a gasar bayan ta samu nasara a kan kungiyar kwallon kafa ta kasar Giunea da ci daya da nema.
Najeriya ta buga wasan ta na biyu ne da kasar Guinea a ranar Laraba, kuma ta zura kwallo daya mai ban haushi a ragar kasar Guinea a wasan da suka buga a wani filin wasa da ke jihar Alexandria da ke kasar Masar,
Dan wasan kungiyar Super Eagles, Kenneth Omeruo, ne ya saka wa Najeriya kwallon da ta ci a minti na 73 da take wasa.
Wannan shine wasa na biyu da Najeriya ta buga a gasar, kuma ta samu nasara a dukkan wasannin.
Samun nasarar kungiyar Super Eagles a wannan wasa, ya bata daar hada maki shida a rukuni na biyu da take tare da kasashen Guine, Burundi da Madagascar.
Super Eagles ta samu nasara ta farko a wasan da ta fara buga wa da kasar Burundi a ranar Asabar. Dan wasan gaba na kungiyar, Edion Ighalo, ne ya saka wa Najeriya kwallo daya tilo da ta ci kasar Burundi.
A ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, ne Najeriya za ta buga wasa na uku da kasar Madagascar a filin wasa na Alexandria.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng