Me Yasa Kasar Saudiyya Ke Narka Makudan Kudade a Harkar Wasanni? An Samu Cikakken Bayani
- Kasar Saudiyya ta na ci gaba da narka biliyoyin daloli a harkar wasanni da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar don rage dogara da danyen mai
- Yarima Mohammed Salman ne ya fadada harkar wasanni a kasar domin shirinsa na 'Cimma muradun Saudiyya a 2030'
- Kasar Saudiyya ta mallaki kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United, ta sayi manyan 'yan wasa, ta kuma shirya wasannin kokowa da 'golf'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kasar Saudiyya - Kashe biliyoyin daloli a harkar wasanni na daga cikin shirin 'Cimma muradun Saudiyya a 2022' wanda yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ke jagoranta.
Manufar shirin 'Cimma muradun Saudiyya a 2022' shi ne samar da wasu hanyoyin kudaden shiga don rage dogaro da danyen mai da siminti, tare da daga darajar Saudiyya a idon duniya.
Da yawa daga cikin 'yan adawa a Saudiyya na ganin wannan a matsayin 'almubazzaranci da kudi, tare da zargin masarautar kasar da yin amfani a hakan don boye zaluncin da take yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hannu daya kuma, wasu na ganin yarima Mohammed ya kawo wannan tsarin ne don habaka tattalin arzikin kasar Saudiyya, Business Insider ta ruwaito.
Ga abubuwan da ya kamata ku sani
Kasar Saudiyya wacce ta kasance gagara-badau a haƙa da safarar danyen mai, ta karkata akalarta zuwa harkokin wasanni, kamar kwallon kafa, wasan 'golf', tseren mota da sauran su.
Saudiyya a harkar kwallon kafa
A watan Oktoba 2021, asusun saka hannun jari na gwamnatin Saudiyya (PIF) ya fitar da dala miliyan 372 don sayen kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United bayan watanni 18 ana ciniki.
A watan Janairu 2022, Ronaldo ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, hakan kuma ya jawo wasu manyan 'yan wasan duniya sun koma buga wasa a kasar Saudiyya.
A watan Yuni, kasar Saudiyya ta samu nasarar farauta 'yan wasa kamar Karim Benzema, Neymar Junior, Sadio Mane da sauran su, wadanda ke taka leda a gasar kofin kasar.
Saudiyya a harkar wasannin 'golf'
A watan Yunin da kasar Saudiyya ta sayi Newcastle United, asusun PIF ya kuma fitar da dala biliyan biyu don gudanar da gasar 'LIV Golf'.
Saudiyya ta yi nasarar jawo ra'ayin manyan 'yan wasan 'golf' irin su Mickelson, Dustin Johnson da Brooks Koepka, wadanda suka shiga gasar da zummar samun kyautar dala miliyan 405.
A shekara biyu kawai, gasar LIV golf ta zarce ta PGA Tour, inda a watan Yuni aka hade gasar biyu a waje daya, karkashin asusun PIF, wanda ya zama babban ci gaba ga Saudiyya.
Saudiyya a harkar wasan kokowa ko tseren mota
Ba iya kwallon kafa da wasan 'golf' kasar Saudiyya ta tsaya ba, domin ta kashe gwamman miliyoyin daloli a harkar wasannin kokowa da motsa jiki.
Ko a shekarar 2021, sai da Saudiyya ta dauki nauyin manyan wasannin kokowa wanda har aka gayyaci Joshua, da gasar WWE da wasan tseren mota na 'Formula 1'.
Yarima Mohammed ya yi martani kan masu suka
Yarima Mohammed mai jiran gado, ya mayar da martani kan masu zargin cewa yana barnatar da dukiyar kasar wajen shirya wasannin da ba zasu yi wa kasar wani tasiri ba.
Sai dai a zantawarsa da Fox News, Yarima Mohammed ya ce shi ko a jikinsa, saboda:
"Na samu karin kudaden shiga na GDP har kaso daya daga harkar wasanni, kuma ina fatan ya kai 1.5%. Duk abin da za su kira ni da shi su kira, ba zan samu ba sai na cimma burina."
Kalamann yariman na nuni da cewa kasar Saudiyya ta shiga harkar wasanni don bunkasa tattalin arzikin ta.
An yi wa Tiwa Savage fashi da tsakar rana a Landan
A wani labarin kuma, kunji cewa shahararriyar mawakiyar Najeriya Tiwa Savage ta gamu da'yan kwanta-kwanta a birnin Landan, kuma sun yi mata fashi da tsakar rana.
Mawakiyar ce ta sanar da hakan a shafinta na Instagram, tare da ɗaukar hoto a dai dai inda abin ya faru.
Asali: Legit.ng