Kano: An Nana Wa Onana, Yamalash Ya Magantu Kan Fashin Bakin Wasanni da Harshen Hausa, Ya Sha Mamaki

Kano: An Nana Wa Onana, Yamalash Ya Magantu Kan Fashin Bakin Wasanni da Harshen Hausa, Ya Sha Mamaki

  • Abubakar Isa Dandago, mai fashin baki a harkokin wasanni a harshen Hausa ya bayyana yadda ya tsinci kanshi a harkar
  • Dandago wanda aka fi sani da 'Yamalash' ya fara fashin bakin ne tun shekarar 2019 tare da abokinsa Abba Tangalashi
  • Dandago ya ce fara wannan fashin baki ya saka mutane da dama fara sha'awar fara kallon kwallon kafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mai fashin baki a harkar kwallon kafa da harshen Hausa, Abubakar Isah Dandago ya bayyana dalilin da ya fada harkar fashin baki.

Dandago wanda aka fi sani da Yamalash dan asalin jihar Kano ne kuma dan jarida a gidan Rediyon Faransa.

Kara karanta wannan

"Yan sanda sun yi garkuwa da ni, sun karbi Naira miliyan 1 kudin fansa", cewar Mr Soyemi

Yamalash ya magantu kan yadda ya sauya tunanin masu sha'awar kwallon kafa
Yamalash ya magantu fashin bakin harkokin wasanni a harshen Hausa Hoto: Abubakar Isa Dandago.
Asali: Facebook

Yaushe Yamalash ya fara fashin baki?

Dandago ya fara aikin jarida a gidan rediyon Freedom kafin barinta a shekarar 2012 inda ya koma gidan rediyon Faransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yamalash ya yi kaurin suna ne tun lokacin gasar kofin duniya a shekarar 2022 a Qatar.

Sai dai ya shiga zukatan mutane ne bayan ya yi fashin baki kan wasan Manchester da ya ke cewa 'An nana wa Onana'.

Yayin hira da jaridar Daily Trust, Yamalash ya bayyana yadda shi kanshi ya ke mamakin irin abin da ya ke yi.

Ya ce:

"A shekarar 1997, na fara sha'awar kwallon kafa inda na fara goyon bayan Manchester United, mutane su na yawan kokwanton kasancewata dan Manchester ganin yadda na ke musu ba dadi a fashin baki.
"Na fara fashin baki a 2019 a gidan rediyo a Kano tare da abokina Isma'il Abba Tangalashi wannan shi ne farkon abin da kawo mu yau.

Kara karanta wannan

"Sha'awa ce": Yadda farfesan jami'ar ABU ya kama aikin walda a matsayin sana'a

"A dalilin haka ne ma gidan talabijin na wasanni, 'Super Sport' su ka gayyace mu don yin fashin baki a harshen Hausa a gasar cin kofin duniya a Qatar."

Wane gudunmawa ya bayar a harkar kwallo?

Yamalash ya kara da cewa duk lokacin da zai yi fashin bakin kawai kalmomin zuwa su ke yi saboda ba ya shirya wa ko rubuta wani abu.

Ya ce dalilin wannan fashin baki a harshen Hausa mutane da dama da ba sa sha'awar kallon kwallon kafa sun fara nuna sha'awa saboda irin yadda ya ke yin fashin baki a harshen da su ke sauraro.

Ya kara da cewa har a kasashen waje da ke amfani da harshen Hausa su na kiransa kan irin yadda ya ke kayatar da su, cewar Independent Post.

Ya kara da cewa:

"Saboda magoya baya na, musamman na ke samun lokaci don yin fashin bakin saboda in kayatar da su a matsayinsu na magoya baya na.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashi wata 6 a gidan kaso saboda satar maggi da sabulu, Alkali ya ba shi zabi

"Wani lokaci ina yi a cikin gida na ko sutudiyon abokai na ko a cikin mota ko kuma duk inda na samu zarafin yi."

'Yan wasan Afirka da su ka fi shura a gasar Firimiya

A wani labarin, akwai zaratan 'yan wasan kwallon kafa da su ka yi tashe ko kuma har yanzu su ke buga gasar Firimiya ta Ingila.

A wannan rahoto, mun jero muku 'yan wasan Afirka takwas wadanda su ka fi shura a gasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel