'El Clasico': Jerin Abubuwa 3 da Su Ka Lalata Armashin Wasa Mafi Daraja a Duniyar Kwallon Kafa

'El Clasico': Jerin Abubuwa 3 da Su Ka Lalata Armashin Wasa Mafi Daraja a Duniyar Kwallon Kafa

A gobe Asabar ce 28 ga watan Oktoba za a kece raini tsakanin Barcelona da Real Madrid a mafi shaharar wasa da aka fi sani da 'El Clasico' a filin wasa na Barca na wucin gadi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Duk da cewa wasan wacce aka fi sani da ‘El Clasico’ ita ce tafi ko wacce zafi a duniya, a yanzu ta rasa wasu abubuwa da ke kara mata armashi.

Jerin abubuwan da su ka rage martabar wasan 'ElClasico'
A shekarun baya, 'El Casico' ta fi ko wace wasa buguwa. Hoto: ESPN.

Real Madrid, bayan wasanni 10 ta na bai wa Barca maki 1 tak a teburi yayin da kungiyar kwallon kafa ta Girona ke saman teburi da maki 28.

Sai da a yanzu wasan ta sauya saboda raguwar martabarta saboda wasu dalilai idan aka kwatanta da shekarun baya, cewar SportsBrief.

Legit Hausa ta tattaro muku abubuwa uku da su ka rage martabar ‘El Clasico’ a yanzu:

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Rashin Ronaldo ko Messi

Gwagwarmayar da ke tsakanin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi shi ya kara wa wasan armashi a shekarun baya.

Amma a yanzu dukkansu sun bar kungiyoyinsu na baya, wanda ya yi tasiri wurin kashe martabar wasan a idon ‘yan kallo.

Da wahala a samu wasan kwallon kafa da za a hada shararrun ‘yan wasa guda biyu kamar Messi da Ronaldo.

Ronaldo ya sha kwallaye 20 a wasanni 34 a kan Barca, yayin da Messi ya sha kwallaye 26 a wasanni 47 kan Madrid, Transfermarkt ta tattaro.

2. Rashin ‘yan wasa masu ban sha’awar kallo

A shekarun baya, ‘El Clasico’ na dauke da ‘yan wasa masu ban sha’awar kallo a cikin fili wanda su ke kara wa wasan armashi saboda yanayin halayensu.

Daga cikin ‘yan wasan da ma su horas da su akwai Jose Mourinho da Pep Guardiola da Pepe da Ramos da Puyol da Dani Alves da sauransu.

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 7 da Dukiyar Naira Miliyan 25 a Wata Babbar Kasuwa, Gwamna Ya Yi Martani

Kasancewar Mourinho a matsayin kocin Madrid ya kara wa ‘El Clasico’ armashi a duniyar wasanni musamman irin yadda ya ke alfahari da kasancewarshi ‘The Special One’.

3. Raguwar Ingancin wasan

A shekarar 2010, Barca ta lallasa Madrid da ci kwallaye biyar da babu wanda ba za a taba mantawa da wannan wasan ba saboda armashinta.

Sannan wasan da Madrid ta ci Barca da kwallaye biyu da daya a gidan Barca a shekarar 2012 na daga cikin wasannin da su ka makale a kwakwalen ‘yan kallo.

A wancan lokaci, Barca na da manyan ‘yan wasa kamar su Valdes da Puyol da Xavi da Iniesta da Messi da Busquets da Pique da sauransu.

Yayin da Madrid ke da Ronaldo da Casillas da Pepe da Ramos da Benzema da Marcelo da Ozil da sauransu.

Messi ya dara Ronaldo a cin kofuna

Kun ji cewa, Lionel Messi ya haura Cristiano Ronaldo a yawan cin kofuna a duniya kamar yadda aka ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Karin Bayani a Kan Jerin Ma'aikatan da Za a Datse Albashinsu

Messi a yanzu haka ya koma kasar Amurka da buga kwallo yayin da Ronaldo ke kasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.